Shaye-shaye da illolinsu ga matasa, lafiya da zamantakewa

Spread the love

Daga BILKISU YUSUF ALI PhD

Shaye-shaye na cikin manyan matsalolin da ke addabar al’ummomi a duniya, musamman matasa. Matsalar tana shafar lafiyar jiki da ta kwakwalwa da ilimi da tattalin arziki da tsaro da zamantakewar al’umma. Wannan rubutu ta yi  nazari kan ma’anar shaye-shaye da nau’o’insu, abubuwan da ke jawo matasa shiga shaye-shaye, illolinsu ga lafiyar mutum da zamantakewa, tare da hanyoyin kariya da magance matsalar. Bincike ya nuna cewa haɗin gwiwar iyaye da malamai da shugabannin addini, gwamnati da al’umma yana da muhimmanci wajen rage wannan matsala.

Gabatarwa

Matasa su ne ginshiƙin ci gaban kowace al’umma. Idan aka ba su ingantacciyar tarbiyya, ilimi da lafiya, za su zama jagororin gobe. Amma idan suka fada cikin shaye-shaye, hakan na iya lalata rayuwarsu da makomarsu. A yau, shaye-shaye sun zama babban ƙalubale a ƙasashe da dama, ciki har da Najeriya. Matsalar tana haddasa ƙaruwar laifuka da rashin tsaro da rushewar iyalai da rashin aikin yi da taɓarɓarewar tattalin arziƙi.

Ma’anar shaye-shaye

Shaye-shaye na nufin amfani da miyagun ƙwayoyi ko wasu abubuwa masu sa maye ba bisa umarnin likita ba ko kuma amfani da su ta hanyar da ke cutar da lafiyar mutum.

Nau’o’in shaye-shaye

Wasu daga cikin abubuwan da ake yawan amfani da su sun haɗa da:

Giya

Taba sigari

Tramadol da makamantansu idan ana amfani da su ba bisa umarnin likita ba

Cannabis (wiwi)

Codeine idan ana amfani da shi ba bisa umarnin likita ba

Hodar iblis (cocaine)

Heroin

Methamphetamine

Shan abubuwan da ke haddasa maye ta wasu hanyoyi kamar kashin ƙadangare da sukudayin da shaƙar kwata da sauransu. 

Abubuwa da dama ne ke zama wata sila ta jefa matasa wannan mummunar ɗabi’a ta shaye-shaye. Daga cikin waɗannan hanyoyi awai: 

Rashin  bayar da tarbiyya ga iyaye

Babban matsala da kan jefa matsa cikin mummunar ɗabi’a ta shaye-shaye akwai sakacin iyaye wurin bayar da tarbiyya yadda ya dace ga iyalansu. Uba shi ne ke da alhakin kula da uwa da ɗanta da saka ido wurin tabbatar da sun samu kulawa. Sai kuma uwa ita da take tare da ɗanta a kullum ya kamata ta fara zama mai tarbiyya sannan ta tsaya ta tabbatar da kula da iyalanta. Rashin kulawar iyaye na iya sa matashi ya shiga mummunar ƙungiya.

Mummunan tasirin abokai

Yana daga cikin haƙƙin iyaye  da malaman makaranta sa ido ga abokanan da yaransu suke ta’ammali da su da kuma tsawatarwa. Sai an sa ido sosai akan abokai. Matasa da yawa suna fara shaye-shaye ne saboda kwaikwayon abokai.

Rashin aikin yi

Zama babu aiki na iya sa wasu shiga shaye-shaye. Don haka rashin abin yi babbar barazana ce ga matasa don da dama wannan ya jefa su a harkar shaye-shaye.  

Talauci

Talauci da matsin rayuwa na iya ƙara haɗarin faɗawa cikin amfani da miyagun ƙwayoyi. Matasa da suka taso cikin  talauci sun fi faɗawa wannan mummunar ɗabi’a ta shaye-shaye. 

Rashin ilimi

Jahilci babbar matsala ce kuma shi ne musabbabin faɗawa daga wannan mummunar ɗabi’a ta shaye-shaye. Sannan rashin sanin illolin shaye-shaye yana sa wasu su gwada su.

Matsalolin tunani

Matsalolin damuwa da  baƙin ciki da wasu matsalolin tunani na iya sa mutum ya nemi mafita ta hanyar shaye-shaye. Sau tari masu matsalar kwakwalwa ko dai wadda shaye-shayen ya illata kwakwalwar ko kuma wadda yake ɗauke da matsalar tuntuni. 

Sauƙin samun miyagun ƙwayoyi

Miyagun kwayoyi suna da sauƙin samuwa musamman ma a wurin waɗanda suke ta’ammali da su, haka masu shaye-shaye suna da zumunci na yadda ko da kuwa ba kuɗi ana iya bayar kyauta ko rance. Don haka kwayoyi suke da saurin samuwa da yaɗuwa. 

Za mu cigaba sati mai zuwa insha Allah.

By ukarofi

Leave a Reply