Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Masu harkar gine-ginen gidaje a Nijeriya sun yi gargaɗin cewa tashin farashin siminti na ƙara tsananta matsalar rashin gidaje mai sauƙin haya ko saya a ƙasar, yayin da Hukumar Kula da Gasa da Kare Haƙƙin Masu Sayayya ta Tarayya (FCCPC) ke gudanar da bincike kan yadda ake ƙayyade farashin siminti.
Binciken kasuwa ya nuna cewa farashin buhun siminti mai nauyin kilogiram 50, wanda ake sayarwa tsakanin N9,300 zuwa N9,700 a watan Janairun 2026, ya haura zuwa kusan N15,000 a wasu wurare zuwa watan Yulin bana.
Wannan ƙarin farashi na zuwa ne a daidai lokacin da masu gine-gine ke fama da hauhawar kuɗin ruwa, tsadar makamashi da kayan gini, da kuma raguwar ƙarfin jama’a na sayen kayayyaki. Hakan ya ƙara musu kuɗin gudanar da ayyukan gine-gine, ya rage ribarsu, tare da ƙara wahalar samar da gidaje masu sauƙin kuɗi.
Manajan Daraktan Legendary Foreshore Construction, Mista ɓictor Ameh, ya ce masana’antar gine-gine na fama da sauyin kuɗaɗen gudanar da aiki, inda farashin buhun siminti tsakanin N13,500 zuwa N15,000 ke kara jefa ayyukan gine-gine cikin mawuyacin hali. Ya ce da dama daga cikin masu gine-ginen na dogaro da rancen bankuna wajen gudanar da ayyukansu, lamarin da ya sa ƙarin farashin kayan gini ya fi yi musu nauyi saboda tuni kuɗin rance ya yi tsada.
Ameh ya yi kira da a kara zuba jari a dukkan sassan masana’antar siminti, tare da ɗaukar matakan rage kuɗin wutar lantarki da man fetur, domin rage kuɗin samar da siminti da kuma farfaɗo da ɓangaren gine-gine.
Shi ma Shugaban ƙungiyar Masu Kasuwar Jari da Masu Kimanta Darajar Kadarori (Association of Capital Market and ɓaluers), Chudi Ubosi, ya ce ƙara yawan masu zuba jari da shigowar ƙarin kamfanoni cikin harkar samar da siminti na iya taimakawa wajen daidaita farashin. A cewarsa, ɗimbin albarkatun farar dutse da Nijeriya ke da su na samar da damar ƙara zuba jari da gasa a masana’antar siminti.
Ubosi ya gargaɗi cewa tsadar siminti na haifar da tasiri mai yaɗuwa a tattalin arziki, musamman a masana’antu, gidaje, kasuwanci da harkar otel-otel. Ya ce, “ ’yan Nijeriya ba sa iya samun gidaje masu kyau saboda matsalar tsadar haya.”
Gargaɗin masu gine-ginen na zuwa ne yayin da FCCPC ke binciken bambancin farashin siminti a Nijeriya da na wasu ƙasashen Afirka. Sai dai masu ruwa da tsaki a masana’antar sun buƙaci hukumar ta yi bincike mai faɗi, maimakon mayar da hankali kan farashin siminti kaɗai wajen gano dalilan bambancin farashin.
