Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
’Yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe Alhaji Garba Buba, shugaban jam’iyyar APC na mazaɓar Rantan da ke ƙaramar hukumar Bebeji a Jihar Kano.
Rahotanni sun ce maharan sun shiga garin Rantan ne a daren Lahadi, inda suka buɗe wa jama’ar garin wuta, lamarin da ya yi sanadin mutuwar wani mazaunin garin mai suna Sulaiman Zunduma.
Wani mazaunin garin, Hamza Isah Rantan, ne ya tabbatar da faruwar harin a wani saƙo da ya wallafa a Facebook, inda ya yi ta’aziyya ga iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su.
Ya ce Alhaji Garba Buba ya samu harbin bindiga a yayin harin, kuma daga bisani ya rasu a wani asibiti da aka garzaya da shi domin neman agajin lafiya.
Hamza ya ƙara da cewa Sulaiman Zunduma, wanda shi ma maharan suka harbe, ya mutu nan take sakamakon raunukan da ya samu.
A cikin saƙon nasa, Hamza ya ce:
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un. A daren Lahadi ne ’yan bindiga suka kai hari garinmu na Rantan, inda suka harbe Alhaji Garba Buba, shugaban APC na mazabar Rantan, wanda daga bisani ya rasu a asibiti. Sun kuma kashe wani mazaunin garin, Sulaiman Zunduma.
“Allah ya gafarta musu kurakuransu, Ya kuma bai wa waɗanda suka jikkata lafiya.”
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar ’yan sandan Jihar Kano ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan harin ba.
Harin ya faru ne sa’o’i kaɗan bayan ceto Sarkin Noman Jihar Kano, Alhaji Yusuf Nadabo Chiromawa, wanda wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da shi a garin Chiromawa da ke ƙaramar hukumar Garun Malam.
Rahotanni sun ce mutane biyar sun samu raunukan harbin bindiga a yayin harin, wanda aka ce ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na daren Asabar.
