Na hannun daman Wike, tsohon mataimakin shugaban PDP na ƙasa, Dan Orbih ya rasu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Sanannen na hannun dama ga Ministan Abuja Nyesom Wike kuam tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa reshen Kudu maso Kudu, Cif Dan Orbih ya rasu.

Marigayi Orbih ya rasu ne a ranar Litinin, 31 ga Agusta, 2026, a cewar wata sanarwa da iyalansa suka fitar. Iyalan sun sanar da haka ne a sanarwar da ke ɗauke da sanya hannun Francis Udukhomoi Orbih a madadinsu, inda suka bayyana al’amarin a matsayin babban rashin da ya jefa su cikin jimami.

“Cikin alhini da ƙunci da yardar da ikon Ubangiji Maɗaukaki, iyalan Chief M.C.K. Orbih na sanar da rasuwar ɗanuwanmu, miji, Uba kuma kawu, Chief Daniel Osi Orbih, wanda ya rasu a ranar Litinin 31 ga Agusta, 2026”, inji sanarwar.

Orbih, wanda ya rasu bayan shafe shekaru 84 a duniya, ya kasance na hannun dama ne ga Wike a harkar siyasa kuma jigo daga cikin fagen siyasar Kudu maso Kudu na jam’iyyar PDP.

Ya kuma taka muhimmiyar rawa wajen tafiyar da harkokin jam’iyyar a Jihar Edo State kuma ana ɗaukar sa a matsayin ɗaya daga cikin masu na hannun dama masu biyayya ga Wike yayin rikicin cikin gida ya dabaibaye jam’iyyar PDP.

Haka kuma, marigayin ya rayu da matarsa Misis Florence Orbih; ‘ya’yansa mata, Mis Winifred Anwosiobor Orbih da Dakta Mildred Omonemi Orbih; ‘yan uwansa maza da mata da wasu shaƙiƙai. Iyalan nasa sun kuma roƙi al’umma da su sanya shi cikin addu’o’insu yayin halin jimamin rashinsa.

By Babaji

Leave a Reply