
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC, ta yi kira ga tsohon gwamnan Jihar Bayelsa, Timipre Sylva wanda aka ayyana a matsayin wanda ake nema kan zargin hannu a badaƙalar Dala miliyan 14.86 da ya je gabanta domin amsa wasu tambayoyi.
Kakakin EFCC, Dele Oyewale ne ya bayyana haka yayin tsokaci kan zargin iƙirarin Sylva na cewa hukumar ta fi karkata zuwa ga yi wa Jam’iyyar APC aiki a madadin tsayawa da ƙafarta a matsayin cibiyar ƙasa.
A ranar Litinin ne dai tsohon gwamnan ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC a hukumance, inda ya ce ya aike wa EFCC kwafin takardar barin jam’iyyar tare da zargin hukumar da yin aiki a matsayin reshen da ke ƙarƙashin jam’iyyar mai mulki.
Tsohon Ƙaramin Ministan Albarkatun Man Fetur ɗin ya kuma zargi APC da sauka daga manufofin da aka kafa ta domin su, sannan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ba wa ‘yan Nijeriya kunya.
Tun a shekarar 2025 ne EFCC ta ayyana Sylva a matsayin wanda ake nema bisa zargin sa da hannu a kitsa makirci da tattaunawar rashin gaskiya da suka ƙunshi badaƙalar $14,859,257.
Sannan ficewar tasa daga APC na zuwa ne bayan watanni da aka danganta shi da zargin kitsa hamɓarar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu. Sylva na ɗaya daga cikin waɗanda ake tuhuma da aikata laifuka 13 ciki har da zargin cin amanar ƙasa, laifuka masu alaƙa da ta’addanci, makirci da almundahanar kuɗaɗe daga zargin kitsa juyin mulkin.
Majiyoyi da dama sun nuna cewa Sylva ya bar Nijeriya bayan an bayyana zargin shirin a bainar jama’a. Majiyoyi na kusa da binciken sun ce ya dakatar da shirin koma wa Nijeriya bayan an kai samame a gidansa da ke Abuja kuma an kama wasu makusantansa.
Kazalika, masu bincike dai sun bayyana Sylva a matsayin mai samar da kuɗi ga shirin makircin, inda suka zarge shi da bayar da kusan miliyan N785 ta kamfanin Purple Waves Limited da ke Abuja daga jimillar biliyan N5 da aka ce an tara saboda shirin. Saidai, Sylva ya musanta hannun zargin kifar da gwamnatin, amma za a yanke hukunci ne kan zarge-zargen yayin da aka gudanar da shari’a kan batun.
