
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Taron da aka yaɗa shiryawa sosai a kafafen sadarwa na haɗakar ‘yan ɓangaren adawa a karon farko domin dunƙulewa waje guda yayin tunkarar zaɓen 2027, ya fuskanci koma-baya sakamakon rashin halartar da dama daga cikin jagororin adawa.
An shirya gudanar da taron ne a ranar Litinin, 31 ga Agusta, 2026 a Abuja.
Rahotanni sun ce, ƙungiyar al’umma ta society pressure group G100 da haɗin-gwiwar jiga-jigan marasa rinjaye na Majalisar Wakilai ne suka shirya taron, wanda aka nemi gudanarwa a ɗakin taro na Musa Yar’Adua Centre domin samar da tsarin fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda da kuma kafa gwamnatin shekera huɗu.
Saidai, rashin ganin jiga-jigan ‘yan adawa kamar su tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar na jam’iyyar ADC, tsohon gwamnan Jihar Anambara Peter Obi da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso na NDC da tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi, ya sanya rashin armashi ga taron.
Haka kuma, wakilan jam’iyyu ba su bayar da wani bayani ba a hukumance game da dalilan da suka sanya ba a ga jiga-jigan ‘yan adawar ba.
Duk da haka an samu halartar da dama daga cikin mambobin sauran jam’iyyu kamar su Social Democratic Party (SDP), Peoples Redemption Party (PRP), Democratic Leadership Alliance (DLA) da kuma Allied Peoples Movement (APM).
Waɗanda suka samu halarta sun haɗa da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar SDP Frins Adewole Adebayo da abokin tafiyarsa Dakta Usman Bugaje; ɗan takarar PRP Donald Duke; na DLA Amb. Moses Olusola; da kuma abokin tafiyar na APM Lawal Daura.
Da yake tsokaci a taron Darakta-Janar na G100 kuma tsohon Darakta-Janar na ƙungiyar gwamnonin APC Salihu Mohd Lukman, ya yi gargaɗin cewa cigaba da samun rarrabuwar kai a tsakanin ‘yan ɓangaren adawa ka iya ba wa jam’iyya mai mulki APC damar samun nasara a zaɓen 2027.
