Ranar Hausa: Kalubalen marubuta da masu fina-finai

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A makon nan ne aka gudanar da bikin Ranar Hausa a sassan duniya daban-daban, wanda aka shirya da nufin raya harshen Hausa da al’adun al’ummar Hausawa. An gudanar da wannan biki a jihohi da dama na arewacin ƙasar nan, har ma da maƙwaftan ƙasashe, inda ake da Hausawa masu yawa.

Ana gudanar da wannan biki ne a kowacce ranar 26 ga watan Agusta, inda tsangayun ilimi a manyan makarantu da ƙungiyoyin Hausawa na raya harshe da al’adu, ke shirya bukukuwa daban-daban, da suka shafi raye-raye, waƙe-waƙe, baje-kolin abincin gargajiya da suturun Hausawa na iyaye da kakanni, har ma da wasannin kwaikwayo da ke isar da saƙonni ga al’umma kan wasu matsaloli da ke damun Hausawa, da nufin nusar da shugabanni nauyin da ke kansu da yadda ya kamata a gyara. Sannan kuma ranar, ta kasance a matsayin wata rana da ake ƙalubalantar al’ummar Hausawa domin fito da sabbin bincike da nazarce-nazarce da nufin ƙara haɓɓaka harshen na Hausa.

Shekaru 11 da suka gabata ne wasu fitattun masu amfani da shafukan sada zumunta a Nijeriya suka ƙirƙiro da wannan ranar tare da keɓe kowacce ranar 26 ga watan Agusta a zaman ranar da za a riƙa gudanar da wannan biki. Harwayau, an keɓance wannan rana ne saboda muhimmancin da take da shi a tarihin harshen Hausa domin tunawa da ranar da aka ƙirƙiro haruffan “ƙ” da “ɗ” da “ɓ” wanda babu su a haruffan Turanci.

Bincike ya nuna cewa, an fara ayyana wannan rana ne a shekarar 2015, bayan da wani ɗan jarida Abdulbaƙi Aliyu Jari da wasu abokansa na shafukan sada zumunta suka ayyana ranar a matsayin Ranar Hausa, don masu magana da Harshen Hausa su haɗu su tattauna cigaba da ƙalubalen da harshen ke fuskanta a ƙarni na 21. An fara bikin farko a shafukan sada zumunta musamman ta manhajar Twitter wanda yanzu ake cewa ɗ, inda mutane ke raya ranar wajen ilimantar da kawunansu karin magana masu sarƙaƙiya da ake da, su a harshen Hausa, ko kuma wasu kalmomi da ke isar da saƙonni masu muhimmanci ga masu magana da harshen Hausa. A kowacce shekara idan ranar ta zagayo ma’abota shafukan sada zumunta na yin amfani da tambarin #RanarHausa domin tattaunawa da yin muhawara. Kafin daga bisani a fara shirya taruka na zahiri don ƙara bunƙasa bikin ranar.

A bana dai, an gabatar da gangamin bikin Ranar ta Hausa ne a birnin Daura da ke Jihar Katsina, a yankin Arewa maso Yamma, inda aka baje-kolin al’adu da gargajiyar Bahaushe tare da gabatar da muƙalu da tattaunawa daga masana harshen Hausa daga sassa daban-daban na ƙasar nan. An ƙiyasta cewa mutane fiye da 400,000 ne suka gudanar da bikin ta Intanet da wasu ƙasashen da Hausawa suke zaune a sassa daban-daban na Duniya irin su Faransa, Amurka, Saudiyya, Kamaru, Ghana, Nijar, da nan gida Nijeriya. Wannan na daga cikin manyan nasarorin da bikin Ranar Hausa ta Duniya ta haifar saboda haɗa kan al’ummar Hausawan Duniya a duk inda suke, ƙarfafa zumunci, da faɗaɗa bincike ta fuskar ilimi.

Masana harshen Hausa da dama na yi wa harshen kallon wani Harshe mai yaɗuwa a faɗin Duniya, inda yanzu haka nazarce-nazarce ke nuna cewa Hausa ce harshe na 11 a faɗin Duniya wajen masu amfani da harshen kuma na ɗaya a Afirka ta Yamma. Kodayake akwai jayayya tsakanin manazarta kan girman harshen Hausa a nahiyar Afirka, inda wasu ke ganin harshen Swahili da ake yi a ƙasashe da dama na yankin Afirka maso Gabas ya ɗara na Hausa wanda ake yi a yankin Afirka ta Yamma, da Afirka ta Tsakiya da ma kusurwar Afirka. Sai dai nazarce-nazarce sun nuna harshen Hausa yana gaba da na Swahili ta fannin yawan masu magana da harshen, inda shi kuma Swahili ke gaba wajen yawa a ƙasashen da ake amfani da shi.

A baya-baya nan, Jamhuriyar Nijar ta ayyana Harshen Hausa a matsayin harshen gudanarwar ƙasa da Gwamnati, wadda wannan mataki ya samu karɓuwa sosai ga al’ummar Hausawa da wasu ƙabilu, duba da bunƙasar harshen a kowace kusurwar ƙasar. Wannan ya sa bikin Ranar Hausa na bana da aka yi a Daura ya karrama Gwamnatin ƙasar Nijar bisa wannan babban gata da ta yi wa harshen Hausa.

Tuni dai su ma manyan kafafe irin su: Facebook da Google suke amfani da harshen Hausa, inda tuni manhajar amfani ta Android da IOS suka shigar da shi cikin harsunan da yake amfani da su. Ko a shekarar 2020 sai da hukumar Lafiya ta Duniya ta sanya Hausa a cikin harsuna guda uku da ta zaɓa domin yaƙi da annobar Korona a Afirka.

Ana fatan harshen Hausa zai samu ƙarin tagomashi nan ba da jimawa ba cikin harsunan da za a riƙa amfani da su a zauren Majalisar ɗinkin Duniya da yayin taron ƙungiyar Haɗa Kan ƙasashen Afirka ta AU da ma ƙungiyar ƙasashen yammacin Afirka ta ECOWAS. Yayin da har yanzu ake buƙatar bincike sosai da nazari a kan harshen Hausa ta hanyar sabbin ƙirƙire-ƙirƙire na zamani domin daga martabar harshen.

Sannan a ɓangaren ƙalubalen da harshen ke fuskanta kuwa masana nazarin harshen Hausa, na ƙorafi kan yadda harshen ke samun komabaya ta fuskar ilimi da nazari, musamman a manyan makarantu inda ake nazarin harshen a matakin digiri na farko da na biyu. Wani malamin harshen Hausa kuma ɗaya daga cikin masu ba da gudunmawa ga cigaban harshen Dr Abdulrahman Aliyu ya koka kan yadda ake samun ƙarancin masu sha’awar yin nazari a harshen Hausa a manyan makarantu, saboda rashin gogewar malaman a fuskar cigaban fasahar zamani da rashin ɓullo da sauye-sauyen da zamani ya kawo a harkar koyarwa. Rashin tsayayyiyar ƙungiya manazarta Harshen Hausa ta ƙasa da ƙasa (Scholars Association).

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Dr Abdulrahman ta rubuta cewa, ‘Sau da yawa nazarin harshen Hausa a matakin karatun digiri na biyu zuwa na uku an tsuke shi kuma an ƙuntace shi ta yadda ɗaliban ba su cika samar da wani bincike na azo a gani da zai tafi daidai da zamani ba, babban abin da zai baka takaici a wannan zamanin a ce wai har yanzu a digiri na biyu ko na uku ana nazarin salo da zubi da tsari da jigo wanann abin takaici ne ƙwarai da ya kamata a ce an wuce shi tuni, a kalli kimiyya da fasaha da ƙirƙire-ƙirƙire da za su taimaki ɗaliban su samar da wani sauyi mai inganci, misali a gargajiyancen ma Shata da sauran mawaƙa sun yi waƙoƙi da suka yi magana kan fasahar samar da ATM da jirgin sama da yanayin ƙasa da albarkatun da ke ciki, to amma da kace za ka yi bincike kan kimiyya da fasahar to, a nan fa za a fara dirama ana gaya ma kai ba sashen Technology kake ba. Ko kuma ba Geography kake ba balle ka yi bayanin kan yanayin ƙasa.

Ya ƙara da cewa, ‘Kaso 70 na malaman da ke koyar da Hausa a manyan makarantun ƙasar nan ba sa tafiya da zamani, abin da suka ɗauka nazarin harshen Hausa ya tsaya ne kacokam kan harshe da adabi da al’ada. Ba su zurfafa bincike kan abubuwan da suka shafi kimiyya da fasaha na zamani da Hausawa ke ta’ammali da su, ba a cika ganin rubuce-rubucensu a sauran fannoni ba, kadan ne kake ganin rubuce-rubucensu a Ingilishi kai hatta harshen Larabci da Faransaci da suke da kusanci sosai da Hausa ba zaka ga malaman Hausa na bayar da gudumuwa a mujallin ɓangarorin ba. Malaman Hausa ba su cika ɗaukar sabon abu ba, da zaran ka zo da sabon abu domin nazari a madadin a jira a gani sai ka ga an fara suka ana kore shi daga nazarin Hausa, hujjar kawai su ba su san abin ba, kuma ba za su bari a sanar da su ba.’

Wani ƙarin ƙalubale kuma shi ne na yadda ake samun shigowar wasu baƙin kalmomi ko gwaranci cikin harshen Hausa, sakamakon yadda waɗanda ba asalin Hausawa ba ke yawa a masana’antar shirya finafinai ta Kannywood, yadda suke magana da wata irin gurɓatacciyar Hausa a cikin finafinan su, kuma hakan na tasiri a maganganun yara masu tasowa. Haka ma wajen rubuce-rubuce da ke fitowa a yanar gizo, matasan marubuta da Hausar ba ta ishe su ba, ko hausar da suke kallo a finafinai ta yi tasiri a kansu, su ma sun koma rubutu da irin wannan bagwariyar Hausa.

Lallai ya kamata masu faɗa a ji a harshen Hausa, da raya harshe da al’adu su tashi tsaye su fara gangamin wayar da kan masu ƙirƙira ta finafinai, marubuta, da masu ɗora bidiyo a zaurukan sada zumunta, domin ƙara tsaftace yadda ake amfani da harshen cikin ayyukan da, suke yi.

By ukarofi

Leave a Reply