Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Babban kotun tarayya da ke Gusau a yammacin yau Litinin ta soke zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC na gundumar Sanatan Zamfara ta Arewa wanda ya samar da Sanata mai ci, Sahabi Ya’u a matsayin ɗan takarar jam’iyyar.
Kotun ta yanke hukuncin cewa tsarin da ya kai ga tsayar da Sanata Ya’u ya saɓa wa tanadin dokar zaɓe ta 2022 da kundin tsarin mulkin APC.
Dakta Sani Abdullahi Shinkafi, wani jigo a APC a Jihar Zamfara ne ya shigar da karar, wanda ya kalubalanci yadda aka gudanar da zaɓen fidda gwanin da kuma sakamakonsa.
Ta hanyar tabbatar da hujjojin mai ƙara, kotun ta soke zaɓen kuma ta umurci APC da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa ta gudanar da sabon zaɓe cikin kwanaki 14 bisa bin doka da oda.
Lauyan mai ƙara, Bello Galadi, ya bayyana hukuncin a matsayin nasara ga dimokuraɗiyya da bin doka.
“Wannan hukuncin ya dawo mana da ƙwarin gwiwa a tsarin shari’armu. Kotun ta bayyana ƙarara cewa dole ne a bi tsarin da ya dace wajen gudanar da zaɓen fidda gwani na jam’iyyu,” Galadi ya shaida wa manema labarai bayan yanke hukuncin.
Ya ce soke takarar Sanata Ya’u ya sa jam’iyyar ta koma fagen daga don sake yin zaɓen fidda gwani.
Da yake mayar da martani ga hukuncin, Dr. Sani Abdullahi Shinkafi ya yaba wa ɓangaren shari’a kan tabbatar da adalci.
“Ina yaba wa kotun bisa tabbatar da cewa an yi adalci. Wannan ba game da mutane ba ne, amma game da ƙarfafa dimokuraɗiyya ta cikin gida a cikin jam’iyyarmu,” in ji shi.
