Mutune 1000 suka kamu da cutar mashaƙo a ƙananan hukumomi 26 na Jihar Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Mutune 1000 suka kamu da cutar mashaƙo a ƙananan hukumomi 26 cikin watanni 8 a Jihar Katsina.

Sakatare na hukumar kula da lafiya a mataki na farko Dr Shehu Kabir ya sanar da haka a hira da manema labarai kan halin da ake ciki game da cutar mashako a Jihar Katsina.

Ya ce akwai alamu kashi 5 bisa 100 na masu ɗauke da cutar sun mutu ko da yake a cewar sa wannan adadi na buƙatar bincike.

Dr Kabir ya bayyana cewa cutar ta mashaƙo ta yaɗu zuwa wasu ƙananan hukumomi,musamman a ƙananan hukumomin Funtua, Kankiya,Bakori, Katsina, Mashi da Daura da suka fi samun masu ɗauke da cutar.

Shugaban hukumar ya ƙara da cewa gwamnnatin Katsina tuni ta ɗauki matakin gaggawar ɗaukar mataki domin kaucewa yaɗuwar cutar.

Yace cutar ta yaɗu a ƙananan hukumomi 29 waɗanda wasu ƙananan hukumomi na da mutane masu ɗauke da cutar suka fi yawa.

Dr Kabir ya bayyana cewa gwamnnatin na nan na gudanar da allurar rigakafi a ƙananan hukumomin Bakori,Charanchi, Funtua, Mashi da Kankiya.

“Gwamnati ta kuma kafa cibiya guda uku a Katsina, Funtua da Daura domin masu buƙatar kularwar gaggawa ga musa ɗauke da cutar,”Inji Dr Kabir Shehu.

Ya ce gwamnati ta samar wa jami’an lafiya magungunan na yau da kullum wanda zai kare mutane ɗaukar cutar.

Haka kuma gwamnati ta horas da jami’an lafiya Kan sanya ido da yadda za su ɗauki mataki na gaggawa da gano ɓulla da kai rahoto da yadda nan take za a samar da magani ga waɗanda ake zargin sun kamu da cutar.

Cutar mashaƙo na haifar da matsalar numfashi,bushewar makogoro da masassara.

Kan haka Dr Kabir Shehu ya yi kira da hakimai da dagatai da masu unguwanni su taimakawa jami’an kiwon lafiya wajan kira ga al’umma da su kai yaran su wajen allurar rigakafin cutar.

By ukarofi