
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Zakaran ƙwallon ƙafa na duniya, Lionel Messi ya sanar da yin ritaya daga buga wasannin gida ga ƙasarsa Argentina bayan wakiltarta a wasanni guda 207.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Messi ya ce: “Mataki ne mai ƙuna – kuma har yanzu yana ƙuna – amma na fahimci cewa lokacin ya zo. Na rantse muku na kasance mai yin dukkan abin da zan iya (wajen cimma nasarori) – ba a iya ga ‘yan shekarun baya ba da muka lashe komai, hatta ma kafin nan.”
“Na kasance a kodayaushe mai yawan fafutukar samun nasara kuma na bar komai ga wannan rigar a fili, domin sanya ku farin ciki kuma ku yi alfahari da zama ‘yan Ajantina ta hanyar ƙwallon ƙafa,” inji shi.
A cewarsa, lokaci abu ne gajere da ya sa ta kai shi ga matakin jingine takalmansa duk da cewa bai son hakan, yana mai cewa akwai zaƙaƙuran matasa masu tasowa da suka cancanci shiga tawagar ‘yan wasan ƙasar don haka yana da kyau a ba su dama.
Messi mai shekaru 39 ya kuma ce bayan rasuwar mahaifinsa Jorge a wannan watan na Agusta, akwai yiwuwar ya dakatar da cigaba da taka tamola nan ba da jimawa, inda a yanzu ya ajiye wakiltar Ajantina a wasanni.
A shekarar 2005 ya fara wakiltar ƙasar, inda a lokacin ne ya lashe Kofin Duniya na ‘yan ƙasa da shekaru 20. Ya kuma lashe Kofin Duniya na 2022 da kuma kai Ajantina matakin wasan ƙarshe a gasar Kofin Duniya na 2014 da kuma 2026. Ya lashe kofin Copa América sau biyu. Haka kuma, ya zura wa ƙasar ƙwallo 125 a wasanni sama da 200.

