
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Dakarun tsaro sun yi nasarar ceto mutum 10 daga cikin ‘yan hidimar ƙasa na NYSC guda 15 da aka yi awon-gaba da su a yankin Jihar Kogi a ranar Juma’a.
An ceto su ne a ranar Litinin a Dajin Egume da ke Ƙaramar Hukumar Ofu ta jihar, kamar yadda Daraktan Yaɗa Labaran Hedikwatar Tsaro, Manjo-Janar Michael Onoja ya bayyana a wata hira.
Onoja ya bayyana haka ne yayin ganawa da ‘yan jarida a Hedikwatar Tsaro (DHQ) da ke Abuja, inda ya ce ana cigaba da atisayen ganin an ceto sauran ‘yan hidimar da ke koma tare da kamo masu garkuwar da suke da hannu a cikin al’amarin. An yi awon-gaba da ‘yan hidimar ƙasar ne a lokacin da suke tafiya daga Abuja zuwa Jihar Bayelsa bayan kammala karɓar horon sati uku a sansanin NYSC.
A cewar Onoja, jami’an tsaro suna cigaba da gudanar da atisaye a yankin domin ganowa da kuma ceto sauran waɗanda suke hannun ‘yan bindigar, yana mai kira ga jama’a da su kwantar da hankali tare da bai wa jami’an haɗin kai wajen ba su bayanai kan dukkan wani abin zargi yayin ƙoƙarin ceto sauran.
A ƙarshen mako ne ‘yan bindigar suka nemi a biya Naira miliyan 20 ga kowane ɗaya daga cikin ‘yan NYSCn, batun da suka shaida wa wasu daga cikin iyalansu, kamar yadda Manhaja ta ruwaito.
Hakan na zuwa ne yayin da hukumomin tsaro ke cigaba da ƙoƙarin ganin an magance matsalolin garkuwa da wasu manyan laifuka a manyan titina da yankunan dazuka a Nijeriya.
