Sojoji sun tarwatsa sansanin ‘yan ta’adda a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Sojojin Operation Fansan Yamma sun tarwatsa sansanin ‘yan bindiga da kashe ɗaya daga cikin kwamandojin su a sansanin ƙasurgumin ɗan bindiga Muhammad Kachalla Fulani a yankin Matazu.

Haka kuma sojojin sun ƙwato makaman yaƙi da wasu kayan aiki.

Sojojin sun sami turjiya daga ‘yan bindigan lokacin da suka soma fafatawa,sai da sojojin suka zafafa hare haren su da amfani da mayan makaman yaƙi wanda ya tilastawa ‘yan bindigan rantawa a na kare.

Bincike da suka gudanar a dajin,sun gano gawar kwamandan ‘yan bindigan mai suna Smally mai gudanar da ta’addanci a sansanin ƙasurgumin ɗan bindiga Muhammad Kachalla Fulani.

Haka kuma sojojin sun kwato bindiga ƙirar machine gun guda biyu da bindiga ƙirar AK-47 guda biyu, sai ma’ajin harsashi guda 11 da zagayen harsasai guda 180.

Sai babura na hawa guda shida wanda ‘yan bindigan suke amfani da su wajen kai hare hare.

Sojojin za su cigaba da zafafa yaƙar ta’addanci har sai sun kakkaɓe ‘yan bindigan da wurare da suka yi sansani a yankin.

By ukarofi

Leave a Reply