Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Majami’ar Threshing Floor Watchman Assembly (TFWA) Lafiya jihar Nasarawa ta kammala taron yara na shekara ta 2026. Taken taron shi ne: “Yaron da Allah ya taimaka ya yi aiki kuma ya shiga cikin shirin Allah a wannan zamanin.”
Taron ya faro ne tun ranar Laraba na makon da ya wuce, ya kuma ƙare ranar Lahadi da ayyuka daban-daban da yaran suka gabatar.
Ayyukan sun haɗa da haddar ayar Bible da gasar tambayoyi da shirin hira da waƙa da tattaki da wasan kwaikwayo da sauran su.
A ranar karshe yaran sun nuna baiwar Allah da suke da ita ta hanyar jagorantar majami’ar cikin yabo da bauta. Bayan haka sun kuma shiga gasar da ake kira “Dauka ka yi” inda aka bai wa waɗanda suka yi nasara kyaututtuka da lada.
Daga rahoton wakilinmu, iyayen yaran ma sun halarci taron. Sun yabi yaran tare da yin addu’a Allah ya cigaba da ƙara musu girma cikin Ubangiji.
A jawabinsa na nasiha baƙo mai lacca Goodluck Vincent ya ilmantar da yaran kan yadda Allah ke taimakawa yaro ya zama mai aiki a cikin aikin Allah. Yace Allah yana buƙatar su kasance masu aiki da shiga cikin shirin Allah domin ceton zamaninsu da ya cika da zunubi.
Ya kuma yi kira ga iyaye da su riƙa renon ‘ya’yansu bisa hanyar Allah inda ya kawo wasu ayoyin Bible da ke ba iyaye shawara kan hakan.
Vincent ya ƙara ba yaran shawara da su guji abokan banza su kuma nisanci kungiyoyin asiri da kuma kada su nemi kuɗi ta hanyar gaggawa. Ya buƙace su biyayya ga iyayensu su kuma sadaukar da ƙarancin shekarunsu gaba ɗaya wajen hidimar Allah.
Ya ƙara gargaɗin cewa kada su yi wasa da ayyukan makaranta na majami’a kowane mako kamar: ajin yara da darussan makarantar Lahadi da addu’a da azumi da sauransu.
A cikin hira da ya yi da manema labarai Bishop Dr. Ovye John wato babban Bishop na Threshing Floor Watchman Assembly ɗin wanda kuma ake kira “Salvation City” a Lafiya yace: “Sunana Bishop Dr. John Ovye. Yau ne ƙarshe na taron ma’aikatar yara na 2026 wato karo na biyu ana yin shi a matakin taron babba. Allah ya taimake mu da taken: “Yaron da Allah ya taimaka ya yi aiki kuma ya shiga cikin shirin Allah don wannan zamaninsa.’
Mun fahimci cewa Allah ne ya halicci yara cikin hotonsa kuma dole ne su isar da shawarar Allah da aikin sa ga wannan zamanin. Kowane yaro kyauta ce daga Allah ga iyali ga jikin Kristi ga ƙasa ga al’umma da kuma ƙabila. Idan ka ga yaro kasancewar Allah da hotonsa suna can.
Saboda haka dole ne mu horar da yaran daidaitaccen tsarin Allah da manufarsa su bayyana a rayuwarsu. Duk yaron da ba zai iya cika nufin Allah ba a zamaninsa to an lalata makomarsa.
A matsayin mu na majami’a mun gane cewa zamanin gobe shi ne yau. Abin da ka bai wa yaronka yau shine zai fito gobe. Akwai karin magana da ke cewa, ‘Abin da ka shuka shine za ka girba.’
Mu majami’a masu kula da adalci ne. Dole ne mu shuka tsaba ta adalci, gaskiya, tsarki, aiki tuƙuru, da ladabi a cikin wannan zamanin. Wannan shine zai warkar da lalacewar da ke cikin al’umma.
Iyali da ba ta horar da ‘ya’yanta, tana taimakawa wajen lalata kasa. Majami’a da ba ta kara wa mutanenta daraja, tana rage darajar al’umma.
Saboda haka muka kira wannan taron ‘Taron ƙara daraja’. Muna kiransa hangen nesa na sama da aka fassara a duniya.
Biblia ta ce, ‘Yara kyauta ne daga Allah,’ kuma suna domin alamomi da abubuwan al’ajabi. Har sai yaranmu sun zama alamomi da abubuwan al’ajabi, ƙasarmu ba za ta ga sauyi, ci gaba, da girma ba.
Muna addu’a wannan taro ya kawo sauyi a Jihar Nasarawa, a Najeriya, da ma duniya baki ɗaya, cikin sunan Yesu. Amin”. Cewar Bishop John Ovye.
