‘Kada ku shiga’, INEC ta ankarar da al’umma kan shafin ɗaukar aiki na bogi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta gargaɗi ‘yan Nijeriya kan wani bogin saƙo da ya ƙunshi shafin ɗaukar aiki na yanar gizo da ke yawo cikin jama’a cewa hukumar ta fara ɗaukar ma’aikata da horar da jami’an wucin-gadi na zaɓukan 2027.

Manhaja ta ruwaito cewa, INEC ta ce saƙon da ake yaɗawa yana bayani kan cewa an samar da shafin ne don ɗibar ma’aikata, amma ta ce sam ba daga gare ta ba ne. A sanarwar da ta fitar a ranar Litinin, INEC ta ce saƙon, wanda ke cigaba da yaɗuwa acikin al’umma yana tura jama’a zuwa shiga shafin da sunan an fara ɗaukar aiki, inda ta ce shafin ba sahihi ba ne daga wajenta.

Akan haka ne ta yi kira ga jama’a da kada su shiga shafin ballantana su bayar da wasu bayanansu aciki, tana mai gargaɗin hakan ka iya kai mutum ga faɗa wa komar ‘yan damfara ko a yi amfani da bayanansa ta wani salo.

Haka kuma, ta shawarci ‘yan Nijeriya da su riƙa bibiyar sahihan shafukanta domin samun bayanai na gaskiya da suka shafi ɗaukar aiki da batutuwan zaɓe da makamantansu. Ta bayyana cewa, domin neman dukkan wani bayani da ya shafe ta, za a iya ziyartar adireshinta na yanar gizo kamar haka: https://inecnigeria.org.

By Babaji

Leave a Reply