Ba za mu taɓa yin sulhu da ‘yan ta’adda ba – Gwamnatin Tarayya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Lahadi Gwamnatin Tarayya ta jaddada aniyarta ta cewa ba za ta amince ta shiga tattaunawar sulhu da ‘yan ta’adda ba, tana mai cewa lallasa su shi ne kaɗai mafita game da matsalolin tsaro da suka jefa al’umma a ciki a sassan Nijeriya.

Ministar Harkokin Waje, Ambasada Bianca Odumegwu Ojukwu ce ta nanata wannan matsaya a wata hira da ‘yan jarida a taron Ƙungiyar Afirka (AU) karo na 21 da aka gudanar a Luanda da ke ƙasar Angola. A cewarta, matsayar Nijeriya ta bijire wa neman sulhu da ‘yan ta’adda tana nan daram ba tare da wani sauyi ba.

Ministar ta yi wannan furuci ne yayin batun ajandar taron, wadda ke magana kan yadda za a magance matsalolin ayyukan ta’addanci, rikicin tsatstsauran ra’ayi da bayar da kariya ga rikici da kuma ciyar da zaman lafiya a sassan Afirka ta hanyoyin gudanarwa da tallafin kuɗi.

Ta bayyana cewa: “Ba za ka iya tattaunawa da ‘yan ta’adda ba. Ba sa fahimtar tattaunawa ko shiga tsakani; ba za ka iya sauya manufa, ra’ayi ko tunaninsu ba. Yaren da suke fahimta kaɗai shi ne cin galaba akansu, kuma wannan shi ne abin da Nijeriya take ƙoƙarin bayyanawa,” inji ta.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu wakilcin Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima a taron, inda ta bayyana matsayar Nijeriya game da tsaron shiyya. Haka kuma, daga cikin tawagar gwamnatin tarayyar akwai ministar harkokin wajen; takwarata na cikin gida, Bunmi Tunji-Ojo; da Ministan Tsaro, Christopher Musa da dai sauransu.

By Babaji

Leave a Reply