Rundunar tsaron al’umma ta Zamfara ta kama wani likitan ‘yan bindiga

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Rundunar tsaron al’umma ta Jihar Zamfara watau Community Protection Guards (CPG), ta kama wani likita da ake zargin bai wa ‘yan ta’adda da suka samu raunuka, kulawar gaggawa tare da wasu mutane takwas da ake zargi da hannu a garkuwa da mutane, satar shanu, samar da makamai da safarar miyagun ƙwayoyi a jihar.

Kwamandan CPG kuma mataimakin sufeto janar na ‘yan sanda, AIG Dr. Muhammad Shehu Dalijan, mai ritaya, ya bayyana hakan a yau Litinin yayin wani taron manema labarai a hedikwatar ta CPG da ke Gusau.

Dalijan ya bayyana wanda ake zargin a matsayin Ibrahim Mafindi Titus, mai shekaru 32, ɗan asalin Jihar Taraba, wanda ya amsa laifin yin aiki a matsayin mai kula da lafiya ga ‘yan ta’adda.

A cewar kwamandan, Titus ya shafe shekara guda a Gobirawa Chali yana kula da ‘yan bindigar da suka ji rauni a yayin arangama da jami’an tsaro.

Titus ya bayyana cewar ya samu hori ne daga wani kamfani da ke Amurka, watau New Life Company da keda reshe a Kano, kuma wata mata mai suna Ruth daga Jihar Filato ce ta gabatar da shi ga ‘yan ta’addan.

AIG Dalijan ya bayyana cewa Titus ya bayyana wa hukumar sa cewar shine ya yi wa waɗanda suka mutu a wani arangama da jami’an tsaro da aka yi a Gobirawa Chali, an kawo masa ‘yan ta’adda su uku, biyu suka samu tsira yayin da daya ya mutu. Haka kuma bayan harin Gummi, an kawo masa wasu ‘yan ta’adda huɗu don ya yi masu magani.

“Titus ya shaidawa manema labarai cewar akwai wani likitan magunguna a Gobirawa Chali mai suna Bala Likita Chali wanda yake kula da mafi yawan ‘yan ta’adda idan sun samu raunuka,” in ji Dalijan.

Rundunar ta CPC ta bayyana wani Abubakar Malan Ori, mai shekaru 20, daga Kwanar Isa, wanda ya yi ikirarin ya shafe watanni biyar zuwa shida a sansanin shahararren ɗan ta’adda Kachalla Gwaska ɗauke da bindiga ƙirar AK-47.

Ori ya amsa laifin shiga cikin ayyukan garkuwa da mutane da dama inda yace sun amsho jimillar Naira miliyan 226 a matsayin kudin fansa daga waɗanda sukayi garkuwa dasu a Jihohin Zamfara, Naija, Kaduna da kuma Jamhuriyar Nijar.

Ya bayyana cewar ana bashi nashi kason daga cikin kuɗin da aka samu daga Naira 50,000 zuwa Naira 100,000 a kowane aiki.

“Lokacin da muka je aiki, muna tafiya da babura kusan 300. A Gummi mun rasa mutane takwas.” Inji shi

Hakazalika DIG Dalijan ya bayyana cewar rundunar sa ta CPG ta kama waɗanda ake zargin da haɗin gwiwa da ‘yan ta’adda, ciki har da Alhaji Hamisu, wanda ake zargin yana karɓar dabbobin da aka sace; Alhaji Danbala da Alhaji Mallan Kabir, waɗanda ake zargi da sayar da zinare ga Gwaska; da Alhaji Sanusi Kango, wanda ake zargin yana samar wa ƙungiyar ‘yan ta’adda babura.

Wani wanda ake zargi, Aliyu Lawali, mai shekaru 20, daga Dumburum a ƙaramar hukumar Zurmi, ya ce ya shafe shekara guda a sansanin Gwaska wanda, a cewarsa, yana da mayaka sama da 500 da babura 700.

Ya amsa cewa ya shiga cikin wani hari da aka kai a Rijana da ke Jihar Kaduna inda aka sace shanu 600, da kuma wani a Jihar Neja inda aka sace shanu 640 da mutane 10, tare da karbar kuɗin fansar da ta kama daga Naira miliyan 5 zuwa Naira miliyan 6 ga kowane wanda aka ɗauka.

“A Gummi, mun sace shanu 500 kuma mun yi garkuwa da mutane takwas amma Naira miliyan 6 kacal aka biya. An kashe mutane da yawa kuma ni da kaina na kashe uku,” in ji Lawali.

Hakazalika, Mamman Haruna, mai shekaru 30, ya ce ya zauna a ƙarƙashin Kachalla Yellow Mai Bille na tsawon shekara guda kuma ya shiga cikin ayyukan da aka yi a Rijana inda aka sace shanu sama da 500 ta amfani da babura sama da 200.

AIG Dalijan ya ce kamawar ta nuna cewa ‘yan ta’adda suna bunƙasa hanyar sadarwa ga masu basu bayanan sirri a cikin al’ummomi.

“CPG ba wai kawai za ta cigaba da kamo waɗanda ke da bindigogi a cikin daji ba, har ma da waɗanda ke ba su damar shiga kasuwanni, asibitoci da ƙauyuka ta hanyar bada bayanan sirri ga ‘yan ta’addan,” in ji shi.

Ya yi kira ga mazauna yankin da su kai rahoton duk wanda ke sayar da magunguna, kayayyakin maye ko kuma saye da sayarwan shanu da yawa ba tare da wata sahihanci sana’ar sa ba.

Kwamandan ya ce, za a miƙa dukkan waɗanda ake zargi ga hukumomin tsaro da suka dace domin ci gaba da bincike da gurfanar da su.

Rundunar ta CPG ta sake jaddada ƙudirin ta na haɗa kai da hukumomin tsaro na tarayya don wargaza hanyoyin ‘yan ta’adda kafin babban zaɓen 2027.

By ukarofi

Leave a Reply