
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon gwamnan Jihar Bayelsa kuma tsohon Ƙaramin Ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva, ya fice daga cikin jam’iyyar APC a hukumance a wani yanayi da sauya lamuran siyasarsa.
Sylva ya sanar da haka ne a wata takarda mai ɗauke da kwanan wata 31 ga Agusta, 2026, inda ya gabatar da ita ga Shugaban APC na Gunduma ta 4 da ke Ƙaramar Hukumar Brass a Jihar Bayelsa.
A takardar, ya bayyana kansa a matsayin ɗaya daga cikin ‘yan siyasar da suka kafa APC, saidai ya bayyana rashin gamsuwa da tsarin alƙiblar shugabancinta a halin yanzu. Ya yi zargin cewa, jam’iyyar ta sauka daga ainihin manufofin da aka kafa a kai, yana mai cewa salon siyasarta a yanzu ya durƙushe ƙa’idojin mutunci da darajarta a idon al’umma.
A cewarsa, ya ɗauki wannan mataki ne bayan shawarwari da iyalans, makusanta, abokan aiki da masu tausayawa, don haka ya gaggauta barin jam’iyyar mai mulki. Sylva dai ɗaya ne daga cikin ‘yan siyasar da suka samar da APC da ci-gabanta kuma yana daga cikin masu faɗa-a-ji acikinta.
A watannin baya ne aka alaƙanta tsohon gwamnan da zargin yunƙurin kitsa makircin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2025, lamarin da ya janyo cece-kuce da fargabar siyasar a ciki da wajen Nijeriya.
