Daga ALI ABUBAKAR SADIQ
Wani faifan bidiyo na Prof Saleh Pakistan a kafafen sadarwa ya fito ya na kamfen a kan sake zabar Tinubu. Wannan ba laifi ba ne, hakkinsa ne na Dan kasa mai ra’ayin tallatawa ko zaben duk wanda ya ga dama. Abinda ban yarda da shi ba cikin zantukansa shine na kokarin nuna cewa a musulunci lallai ne a yi wa shugaba addua, kuma haramun ne a tsine masa. Wannan fahimta ta su, cewar ba’a la’antar shugaba duk munin zaluncinsa yaudara ce da kwadayi ya assasa ta. Kuma ni ban yi mamakin ganin Saleh Pakistan ya fadi haka ba. Domin a baya ya yi abinda ya fi haka muni.
Na farko ba zamu manta cewa ya tattaro Malaman Izala kaf na Kano a lokacin Ganduje sun je gidan gwamna sun yi wa gwamna solidarity lokacin badakalar zargin cusa Dala. Inda a cikin bayanan sa ya ke cewa “Yadda Allah ya wanke Aisha daga zargin Zina, haka mu ke sa ran Allah zai wanke Mai girma gwamna daga zargin nan (cusa Dala)” Don Allah, wanda a sunan malami zai kwatanta abinda ya shafi Aisha da wanda ya shafi Ganduje, menene kuma abin mamaki idan yayi wani kalami? Koda yake, hakan ya haifar masa da samun gwaggwabar kujerar shugaban hukumar Alhazai na kasa, kujerar da kada mu manta sakamakon zarge-zarge na cin hanci da rashawa da ya mamaye mulkinsa a wajen ne ya tilasta masa murabus a farkon shekarar nan.
Sannan a kokarin tallata gwamnatin, Sheikh din ya kawo labari cewa Imam Ahmad bn Hanbal, na cewa idan da akwai wata addua da zai yi nan take a karba, to, ba zai wa kansa ba sai dai yayi wa shugaba. Ba tantama, hakika Imam Ahmad ya yi gaskiya, domin a duk al’umma babu mai mahimmanci shugaba (ya halatta ko rai a sadaukar wajen shi) amma wane irin shugaba ake nufin? Imam Ahmad na maganar adalan shugabanni saboda mahimmancinsu ga al’umma. Domin idan ya gyaru kowa zai gyaru. Wajibi a yi wa irin wadannan shugabanni addua, saboda su na bin abinda Allah ya umarce su da shi na adalci. Sheikh ya kawo misalin Malaman Saudia yadda su ke yiwa shugabanni addua. A matsayina wanda ya zauna a kasar Saudia, Malaman Saudia na da hakkin yiwa shugabanninsu addua domin sun basu tsaro, sun kyautata harkar lafiya da Ilimi da ayyukan yi ga Yan kasar su. Kowa na morar arzikin Mai da Allah ya hore musu. Amma mu fa?
Maganar cewa ba a yiwa azzalumin shugaba addu’a mara kyau ko zanga-zanga, wani hadin baki ne tsakanin Malaman fada da masu Mulki (wanda ya samo asali tun farko farkon musulunci karkashin daular Umayya), amma ba cikakkiyar koyarwar Musulunci ba ne. Na farko dai kamar yadda duk wanda ya je makaranta (ba sai Malami ba) tun muna Yara cikin jerin littafan farko na fiqhu da ake koyarwar, wato Qawa’idi, shine cewar; “babu ɗa’a ga wani mutum, idan ya shafi saɓa wa Allah.” Sharia kaf ta ginu akan wannan hadisin, domin asalin zancen an zaƙulo shi daga Miskah Al Masabih hadisi na 3696.
Haka nan tarihin musulunci, tun daga Sayyidna Umar, musulmi sun ginu a kan cewa shugabancin da su ka fuskanci akwai alamar zalunci, ko dai ayi bayani, kamar yadda aka titsiye Umar a mimbarin jummu’a don ya yi bayanin inda ya sami gyauto biyu maimakon daya a ganima, ko yadda Abu Dharr ya rika sukar Mu’awiyya harda jawo ayar Tauba 34 wadda ke gargadin shugabanni akan tara Dukiya ba tare da ciyar da talaka ba. Abinda ya sa aka koro shi daga Syria ya dawo Madina Usman na mulki, kuma bai fasa sukar shugabanni kan su yi adalci ba. A karshe Usman ya kore shi daga Madina zuwa Rabatha inda ya mutu. Abu Dharr ne Dan gwagwarmaya na farko a musulunci, kuma kowa ya san kimarsa cikin sahabbai da a wajen manzon Allah.
Akwai irinsu Abdullahi Bn Zubair, Ammar B Yasir, Husain Bn Ali wadanda duk sahabbai ne da suka soki rashin adalcin shugabanni. Sannan cikin tabi’ai mun ga irinsu Said Bn Jubair, Hasan Al Basri, Said Bn Musayyib da sauransu. Musulunci kaf dinsa ya zo yakar zalunci ne, amma saboda Kwadayin Malaman fada sun haramta a soki shugabanni. Sukar shugabanni domin su gyara wajibi ne, ballantana ma wadanda su ka zalunci al’umma su ka kasa tsare rayuka da dukiyoyinsu. Tun a Duniya Allah ya bamu izinin cewa: Q4:146: Allah bã Ya son bayyanãwa da mũnãna daga magana fãce ga wanda aka zãlunta. Kuma Allah Yã kasance Mai ji, Masani.”
Duk da Allah baya son tsinuwa da zagi, Amma idan an zalunci mutum yana da Iko. A karshe mu sani cewa Allah da kansa ya bamu labari cikin suratul Ahzab halascin tsinewa duk wani tsinanne shugaba.
Q33:68 “Yã Ubangijinmu! Ka ba su ninki biyu na azãba, kuma ka LA’ANE su, la´ana mai girma.” Wato har a gaban Allah a ranar lahira, duk shugaba (Mai mulki ko malami) da ya yi umarni, ya halasta ya kuma aikata zalunci kan wadanda aka bashi amanarsu, to tabbas ya cancanci la’ana ta wadanda ya zalunta, nan Duniya da Lahira.
Shin wai malaman mu basa jin kunya ne? A ce hatta Malaman kiristoci na kira a daina zaluntar talaka, a sake masu mara, amma Malaman Izala ku ne gaba wajen tabbatar da dawwamar al’ummarku karkashin talauci da koma baya? Wa iyazu billah!!!
Abubakar mai sharhi kan harkokin yau da kullum ne a Kano
