Daga JOHN WADA a Lafiya
Kwamishiniyar ma’aikatar muhalli da albarkatun ƙasa ta jihar Nasarawa gimbiya Dr. Margaret Elayo ta miƙa ragamar jagorancin ma’aikatar harkokin mata da cigaban jama’a ga sabuwar kwamishiniya Hon. Rebecca Adamu Kpadji.
An gudanar da bikin miƙa mulkin ne a sakatariyar gwamnatin jihar dake Lafiya. Wannan ya kuma nuna farawar sabon jagoranci a cikin ma’aikatar.
A lokacin bikin Dr. Margaret Elayo ta roƙi ma’aikata da shugabannin ma’aikatar da su ba sabuwar kwamishiniyar cikakken goyon bayan da suka ba ta.
Ta jaddada cewa Hon. Kpadji ba baƙuwa ba ce a ma’aikatar harkokin matan domin ta yi ritaya daga aikin gwamnati ba da daɗewa ba. Ta buƙace ta ta ɗauki ma’aikatar a matsayin gidanta inda za ta rungumi kowa ba tare da nuna bambanci ba.
Dr. Margaret ta nuna godiyarta musamman ga gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule bisa damar da ya ba ta na riƙo a ma’aikatar a matsayin kwamishiniya mai kula da ita na wucin gadi. Haka kuma ta yi wa Hon. Kpadji fatan nasara a sabon muƙamin nata.
A jawabinta sabuwar kwamishiniyar Hon. Rebecca Adamu Kpadji ta yaba wa Dr. Margaret bisa jagoranci da kuma yadda ta gudanar da ma’aikatar a lokacin da take riƙe da ita.
Ta jaddada muhimmancin haɗin kai da jajircewa da ladabi da sadaukarwa ga ma’aikata da shugabanni.
Hon. Kpadji ta kuma buƙaci ma’aikata da su haɗa kai da riƙe amana su kuma goyi bayan ma’aikatar domin cimma burinta musamman wajen inganta jin dadin mata da ‘ya’ya da kuma marasa galihu a cikin al’umma.
