Daga UMAR GARBA a Katsina
Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun halaka manyan kwamandoji biyu na wata ƙungiyar ‘yan ta’adda ƙarqashin jagorancin ƙasurgumin ɗan bindiga, Kachalla Muhammadu Filani, a ƙaramar hukumar Matazu ta Jihar Katsina.
Rundunar ta ce an halaka mutanen biyu, Hamisu, wanda aka fi sani da Mamiyo, da Umar Bocho, ne a wani samame da aka gudanar bisa bayanan sirri a kusa da ƙauyen Kogo ranar Litinin, 31 ga Agusta, 2026.
Jami’in yaɗa Labarai na Operation FANSAN YAMMA, Lt. Col. Aliyu Danja, ya ce dakarun Sector 2 sun yi arangama da ‘yan ta’addan a maɓoyarsu, inda aka yi musayar wuta mai tsanani.
Ya bayyana Mamiyo a matsayin fitaccen mai safarar makamai kuma mataimakin Muhammadu Filani, yayin da Umar Bocho ya kasance muhimmin jigo a cikin ƙungiyar.
A cewar rundunar, Kachalla Muhammadu Filani ya tsere daga wurin da raunukan harbin bindiga, yayin da dakarun ke ci gaba da farautarsa da sauran mambobin ƙungiyar.
Rundunar ta bayyana nasarar a matsayin babban koma-baya ga ƙungiyar ‘yan ta’addan, tare da cewa kashe kwamandojin biyu zai rage mata ƙarfin gudanar da ayyukanta tare da kawo cikas ga ayyukan ta’addanci.
