Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kamfanin Mai na Nijeriya (NNPCL) da abokan hulɗarsa a kan Yarjejeniyar Haƙar Mai ta OML 118 sun rattaba hannu kan wasu muhimman yarjejeniyoyin kasuwanci da suka shafi aikin haƙar mai da iskar gas na Bonga Southwest/Aparo da ke zurfin teku.
Ana sa ran matakin zai hanzarta aikin zuwa matakin ƙudurin zuba jari na ƙarshe, wato Final Inɓestment Decision (FID), tare da buɗe ƙofar zuba jarin da zai iya kaiwa tsakanin dala biliyan 15 zuwa 21.
Babban Daraktan Rukunin NNPC Limited, Bayo Ojulari, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, inda ya ce kamfanin tare da Shell Nigeria Eɗploration and Production Company (SNEPCo), Esso Eɗploration and Production Nigeria da Nigerian Agip Eɗploration (NAE), sun kammala rattaba hannu kan kari ga Yarjejeniyar Raba Samarwa (PSC) da kuma Yarjejeniyar Sasanta Rikici (DSA) da suka shafi aikin. Ojulari ya bayyana yarjejeniyoyin a matsayin wani gagarumin mataki na amfani da ɗimbin albarkatun man fetur da iskar gas da Nijeriya ke da su a zurfin teku, yana mai cewa amfanin aikin ba zai tsaya ga samar da danyen mai kawai ba.
A cewarsa, aikin Bonga Southwest/Aparo na da karfin jawo zuba jari tsakanin dala biliyan 15 zuwa 21, tare da samar da kusan gangar mai 175,000 a kowace rana, baya ga iskar gas da ta kai mita cubic miliyan 140 a kowace rana.
Ya ce aikin zai kuma samar da guraben ayyukan yi ga ’yan Nijeriya, tare da kara bunƙasa harkokin cikin gida (local content) a sassan masana’antar man fetur da iskar gas.
Baya ga haka, Ojulari ya ce aikin zai ƙarfafa hanyoyin samar da kayayyaki da ayyuka a cikin gida, tare da samar wa gwamnati ɗimbin kudaden shiga, abin da zai kara tabbatar da matsayin Nijeriya a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙasashen da ke hako mai daga zurfin teku.
Shugaban NNPC ya yabawa Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, kan amincewa da Dokar Tallafin Zuba Jari a Ayyukan Zurfin Teku ta 2026, wadda ya ce ta taimaka wajen samar da yanayin da ya fi jan hankalin masu zuba jari a ayyukan haƙar mai daga teku. Ya kuma yaba wa hukumomin da ke kula da masana’antar, kamfanonin da ke da hannu a aikin da kuma ƙungiyoyin kwararrun da suka taka rawa wajen ciyar da aikin gaba.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na ɗ, Ojulari ya ce rattaba hannun yarjejeniyoyin ya ƙara kusantar Nijeriya da matakin yanke shawarar karshe kan zuba jarin aikin. Ya jaddada cewa manufar aikin ba wai ƙara yawan gangar man da Nijeriya ke samarwa kaɗai ba ce, illa kuma samar da guraben ayyukan yi, bunƙasa masana’antun cikin gida, ƙarfafa hanyoyin samar da kayayyaki da kuma ƙara kuɗaɗen shiga ga ƙasa.
Aikin Bonga Southwest/Aparo na daga cikin manyan albarkatun mai da Nijeriya ke da su a zurfin teku waɗanda har yanzu ba a fara cin moriyarsu gaba ɗaya ba. Ana sa ran kammala aikin zai taka muhimmiyar rawa wajen ƙara yawan man fetur da iskar gas da Nijeriya ke samarwa, tare da taimakawa wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.
A baya, Shugaba Tinubu ya amince da wani rangwamen haraji na musamman domin taimakawa wajen buɗe hanyar yanke shawarar zuba jari a aikin, wanda ake sa ran zai jawo kimanin dala biliyan 20 na zuba jari daga ƙasashen waje zuwa ɓangaren makamashi na Nijeriya.
