An halaka ‘yan bindiga 30 yayin da ‘yan ƙauyen Zamfara suka mayar da martanin hari

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mazauna ƙauyen Birnin Tudu na Ƙaramar Hukumar Gummin Jihar Zamfara a Arewa maso Yammacin Nijeriya, sun ce sun yi nasarar halaka sama da ‘yan bindiga 30 a yayin wani ba-takashi na tsawon kwanaki uku a tsakaninsu a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka farmaki ‘yan ƙauyen. Sun ce maharan, waɗanda suka yi cincirindo akan babura da adadinsu ya haura 100, sun zagaye ƙauyen nasu suka riƙa harbe-harbe.

Da yake zantawa da jaridar Daily Trust bisa sharaɗin a sakaye sunansa, wani ɗan yankin ya ce maharan sun yi musu ziyara ba-zata ne a lokacin da suka shantake game da harkokin sintirin lamuran tsaro a yankin.
“Mun jima muna sanya ido da ƙoƙarin kare kanmu, amma wannan lokaci, mun ɗauka ana kula da komai na lamuran tsaro,” inji shi.

A cewarsa, maharan sun afka musu ne da misalin ƙarfe 10 na safiyar Talata, a lokacin da manoman ƙauyen da dama suka tafi gonakinsu domin gudanar da wasu ayyuka da suka shafi nome abin da suka shuka. “Kafin mu farga da abin da ke faruwa, ‘yan bindigar sun zagaye ƙauyen ta ko’ina. Sun zo ne mutum uku-uku akan babura. Babura sama da 100 ne suka zo, kuma musamman na ƙirga sama da guda 71 daga wurin da nake ɓoye,” inji mazaunin.

Ya bayyana cewa, a lokacin da maharan suka je ƙauyen, sun riƙa yin harbe-harbe tare da fasa shaguna da sace wasu kayayyaki. Akan haka ne ‘yan garin suka mayar da martani akan tserewa, inda ‘yan ƙauyen guda uku suka rasu, sannan wasu kuma suka jikkata daga harbin bindiga da wasu raunuka. Ya ƙara da cewa, ‘yan bindigar sun sake dawowa a karo na biyu yayin da ‘yan garin suke raba batiran fitilu, amma kuma sun sake kare kansu tare da kora su zuwa yankin gabashin ƙauyen.

Wani ɗan yankin ya ce, maharan sun kasance ‘yan daba uku ne – na farko akan babura sama da 70 da ke ɗauke da mutum uku kowanne, na biyu ta zo da dabbobi da ta sato, sai na ukun ke biye da su. Ya ce, bayan ɗauki-ba-daɗi sun yi nasarar halaka sama da ‘yan bindiga 30.

By Babaji

Leave a Reply