Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Wani mummunan Iftila’i ya afku a garin Kaura Namoda ta Jihar Zamfara, yayin da ‘yan bindiga ɗauke da muggan makamai suka kai hari jiya cikin dare, inda suka kashe aƙalla mutum bakwai tare da yin garkuwa da wasu da dama.
A cewar majiyoyin gida, ‘yan ta’addan sun kutsa garin ne da tsakar dare ranar Juma’a kuma suka yi ta’adi ba tare da an dakatar da su ba har zuwa asubahin ranar Asabar, inda suka kai hare-hare a unguwanni daban-daban.
Wuraren da lamarin ya shafa sun haɗa da Tsohuwar Kasuwa, Gangaren Gulbi, Matoyar Tuluna, da wani ɓangare na Ƙofar Zurmi.
Mazauna garin da suka zanta da wakilin mu sun ce maharan sun iso ne da babura masu yawa, suna harbi ba ƙaƙƙautawa suna kuma tilasta shiga gidajen jama’a, inda suka kashe mutum bakwai tare da ɗauke wasu da dama zuwa wani wuri da ba a sani ba.
“Adadin mutanen da aka yi garkuwa da su ba a tantance ba tukuna saboda iyalai na ci gaba da duba ‘yan uwansu da suka ɓace”. In ji wani.
Wani mazaunin garin, wanda ya buƙaci a sakaya sunan sa saboda tsaro, ya bayyana harin a matsayin abin baƙin ciki tare da kuka kan yadda ‘yan bindigan suka yi ta’adi cikin sauƙi.
“Abin baƙin ciki ne yadda aka bari waɗannan ‘yan ta’adda suka yi ta’adi cikin walwala a wannan gari na Ƙaura Namoda”.
“Mun san hukumomi na ƙoƙari, amma muna kira gare su da su ƙara ƙaimi wajen magance wannan matsala”. In ji shi.
Ƙaura Namoda na ɗaya daga cikin ƙananan hukumomin da suka fi fama da hare-hare a Jihar Zamfara kuma ta sha fama da hare-hare akai-akai a ‘yan watannin nan duk da ci gaba da ayyukan soji a yankin Arewa maso Yamma.
Ƙoƙarin samun tabbaci daga rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara bai yi nasara ba a lokacin haɗa wannan rahoto.
Sai dai majiyoyin tsaro sun ce an tura dakarun soji zuwa wuraren da abin ya shafa domin dawo da zaman lafiya da kuma bin sawun maharan.
Haren ya auku ne kusan sa’o’i 48 bayan da sojoji suka sanar da ƙaddamar da sabbin hare-hare kan maɓoyar ‘yan bindiga a yankin Zamfara da Katsina.
Mazauna yankin na roƙon gwamnatin tarayya da gwamnatin Jihar Zamfara ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal da su ƙarfafa tsaro a garin Ƙaura Namoda, wanda a cewar su ya zama mai saukin shigowar ‘yan ta’adda don kai hare-hare akai-akai.
Tuni dai aka binne waɗanda suka rasa ransu a yau Asabar bisa turbar addinin Musulunci.
