‘Yan sandan Nasarawa sun kama mutum uku tare da gano gonar wiwi

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafia

Jami’an rundunar ‘yan sandan Jihar Nasarawa sun kama mutum uku tare da ƙwato adadi mai yawa na busassun ganye da sabbin ganye da ake zargin wiwi ne a ƙaramar hukumar Keana.

Waɗanda ake zargin su ne Aondaver Dominic da Sylvanus Umoor da Peter Tar an kama su ne a ranar 22 ga Oktoba 2026 da misalin ƙarfe karfe 1:00 na rana, waɗanda jami’an sashen binciken manyan laifuka na Jihar SCID a Lafia suka cafke su yayin sintiri a ƙauyukan Sabongida Bature da Gidan Kparev, a garin Kadarko.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar SP Ramhan Nansel a wata takarda da aka ba manema labarai ciki harda wakilin mu yace jami’an sun isa wata ɓoyayyar mafaka da ake zargin ana sayarwa da shan wiwi. Da ganin ‘yan sandan ne sai waɗanda ake zargin suka yi yunƙurin guduwa amma aka cafke su tare da adadi na busassun ganye da ake zargin wiwi ne.

A cewarsa bincike na gaba ya kai jami’an zuwa wani lambu a bayan gidan waɗanda ake zargin inda ake noman wiwin da safarar ta kuma an ƙwato sabbin ganyen da aka girbe da ake zargin gayen wiwin ne.

Yace a yanzu haka an adana dukkan kayan da aka ƙwato domin cigaba da bincike.

A halin da ake ciki, kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Shetima Jauro Mohammed ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike tare da umartar a miƙa waɗanda ake zargin da kayan da aka kwato ga hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi wato NDLEA domin ɗaukar mataki na gaba.

CP din ya buƙaci jami’ai na rundunar da su cigaba da ƙaimi tare da ƙara zage damtse wajen yaƙi da dukkan nau’ikan laifuka a faɗin jihar.

Ya tabbatar wa mazauna yankin cewa rundunar na kare rayuka da dukiyoyi tare da buƙatar jama’a da su cigaba da bayar da ingantattun bayanai akan lokaci ga jami’an tsaro don basu damar cigaba da daƙile ayyukan ɓatagari a faɗin jihar ta Nasarawa baki ɗaya.

By ukarofi

Leave a Reply