Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Gwamnan Jihar Zamfara, Dakta Dauda Lawal, murnar zagayowar ranar haihuwarsa a yau, 2 ga Satumba.
Shugaban Ƙasar ya taya Gwamna Lawal murnar wannan rana, yana bayyana shi a matsayin gwamnan da ya sake farfaɗo da jihar Zamfara tare da kawo sauye-sauye masu inganci a fannoni daban-daban.
Sanarwar na ɗauke da sa hannun Bayo Onanuga, mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, a ranar 2 ga Satumba, 2026.
Shugaba Tinubu ya yaba musamman da ƙoƙarin gwamnan wajen gina ababen more rayuwa, sabunta birane da kuma inganta harkar masana’antu a jihar.
Haka kuma, shugaban ƙasar ya yaba wa Gwamna Lawal bisa faɗaɗa ayyukan gwamnatinsa fiye da samar da ababen more rayuwa, inda ya gyara tare da farfaɗo da makarantu sama da 800, ya ɗauki malamai fiye da 2,000 aiki, ya inganta asibitoci tare da samar da magunguna da sauran kayan aikin lafiya a sassa daban-daban na Zamfara.
Shugaba Tinubu, wanda ke mara wa tsarin ci gaba mai ɗorewa da ya shafi dukkan muhimman fannoni baya, ya ce yadda Gwamna Lawal ke tafiyar da mulki ta hanyar mai da hankali kan fannoni daban-daban na rayuwar al’umma ya dace da manufar samar da ci gaba mai ɗorewa, musamman wajen bunƙasa ƙwarewar jama’a da jari-hujjar ɗan Adam.
Shugaban ƙasar ya ce yayin da Gwamna Dauda Lawal ke bikin zagayowar ranar haihuwarsa, ya haɗa kai da iyalansa, abokansa da kuma al’ummar Jihar Zamfara wajen yi masa fatan samun ƙoshin lafiya da ƙarin ƙarfi, domin ci gaba da hidimtawa jihar da ƙasa baki ɗaya.
