Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe
Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Manoma da masu Kasuwnacin Auduga na shiyyar Arewa maso gabashin Nijeriya Alhaji Sadiq Ado, ya bayyana cewa haɓaka noman auduga da kasuwancin ta zai farfaɗo da durƙusassun masaƙun Nijeriya da suka daina aiki.
Alhaji Sadiq Ado wanda kuma shi ne shugaban ƙungiyar a jihar Gombe ya ce dawo da noman auduga da tallafawa manoman zai haɓaka tattalin arzikin ‘yyan Nijeriya da yawa.
Ado ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa inda taɓarɓarewar da harkar ta yi idan gwamnatoci suka shigo wajen taimakawa manoman harkar za ta dawo daidai domin a har kullum rashin kulawa ke haifar da matsaloli na kowanne irin abu ne.
“Masaƙun Nijeriya da ake da su suka dai na aiki muddin noman auduga ya bunqasa za su farfaɗo musamman idan gwamnati tana son hakan.”
Alhaji Sadiq Ado, ya ƙara da cewa idan aka nemo manoman aka taimaka musu don yin noman hatta cinikakkayyar ta zai dawo irin na da lokacin da Turawa suke zuwa sayen auduga a Nijeriya wanda kuma a duk audugar da ake nomawa babu mai kyawun ta Gombe.
Har ila yau ya ce a shekarun baya shirin nan na gwamnatin tarayya na Anchor Borrowers ya taimaka wajen qara haɓaka harkar noman wanda ba a san yanzu ko wannan gwamnatin za ta ci gaba da shi ba ganin cewa ta yi shiru akai amma da za ta ci gaba da harkar noman auduga ya wuce inda ake tsammani.
Sannan ya ce rashin noma audugar ya sa wuraren gurzar audugar wato Ginery da ake da su sun zama ba sa aiki inda nan ma koma baya ne wajen samar da aikin yi wa matasa.
Daga nan sai ya yi kira ga manoman da ma ‘yyan kasuwar da suke safarar audugar cewa su riƙe harkar da gaskiya domin rashin gaskiya a harkar da yin algus shi ke qara kawo koma baya musamman wajen sayar da ita a kasuwanni domin duk inda ka kai auguda ta Gombe ta fi kyau.
