Masarautar Gaya ta naɗa Munzir Yusuf Ali muƙamin Sarkin Malamai

Mai Martaba Sarkin Masarautar Gaya a Jihar Kano, Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya, ya amince da naɗin Alhaji Munzir Yusuf Ali a matsayin Sarkin Malaman Gaya.

Sanarwar naɗin na ƙunshe ne cikin wasiƙar da masarautar ta fitar mai ɗauke da sa hannun Wamban Gaya, Alhaji Mansur Ibrahim Gaya, da kuma kwanan wata 8 ga Mayun 2024.

Sanarwar ta ce bikin naɗin zai gudana ne a ranar Juma’a, 17 ga Mayu, 2024, da misalin ƙarfe 10 na safe a Fadar Sarkin Gaya.

“Saboda haka ana ba ka shawarar ka ci gaba da shirye-shirye don tabbatar da nasarar wannan naɗin,” in ji sanarwar.