ECOWAS za ta kafa dakarun ko-ta-kwana don yaƙi da ta’addanci a Yammacin Afirka

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ƙungiyar Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka ECOWAS ta ce za ta kafa dakarun ko-ta-kwana domin tunkarar matsalar ‘yan ta’adda masu iƙirarin jihadi da ke tayar da zaune tsaye a ƙasashe daban-daban, kamar yadda shafin intanet na The Nation mai zaman kansa a Nijeriya ya rawaito.

Kwamishinan ECOWAS Abdel-Fatau Musah ya faɗi hakan ne a ranar Talata a Abuja cewa ƙungiyar na buƙatar tara dala biliyan 2.4 ga dakarun, inda ƙasashe mambobin ƙungiyar suka bayar da rabin adadin.

“A yau, Burkina Faso ta zarce Afganistan a matsayin ƙasa mafi fama da ta’addanci a duniya kuma Afirka ta zama gida ga qungiyoyin ta’addanci,” inji Musah.

Shugabannin sojojin Mali da Burkina Faso da Nijar dai sun janye daga ƙungiyar ta Ecowas a farkon wannan shekarar, bayan da suka zarge ta da rashin tallafa musu wajen tunkarar tashe-tashen hankula daga ƙungiyoyin al-Qaeda da IS a tsawon shekaru.