Ɗan Majalisar Tarayya, Isa Dogonyaro ya kwanta dama

Daga BASHIR ISAH

Allah Ya yi wa ɗan Majalisar Tarayya, Isa Dogonyaro, mai wakiltar mazaɓar Garki/Babura a Majalisar Wakilai ta Ƙasa, rasuwa.

Sanarwar rasuwar marigayin ta fito ne ta hannun abokin aikinsa, Mohammed Bello El-Rufa’i, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook da safiyar Juma’a

“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Da safiyar yau muka rasa abokin aiki a Majalisar Wakilai ta Ƙasa, mutumin kirki da ƙwazo.

“Da fatan Allah SWT Ya gafarta masa, Ya kuma sanya shi cikin Aljannatul Firdaus,” in ji sanarwar.