Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano
Shugaba kuma wanda ya kafa Ƙungiyar RED, Alhaji Bello Giɗaɗo Rahaji, ya bayyana cewa yadda ya ga gwamnan su na Jihar Neja Alhaji Mohammed Umar Bago yake tafi da mulki bisa taka-tsantsan da bin diddigi a kan duk wani aiki ko amana da ya bayar da ci gaban al’ummar jihar Neja, wannan abun koyi ne ga gwamnoni da shugabanni da sauran al’ummar Nijeriya.
Domin a cewarsa wannan shi ne zai kawo kyakkyawan cigaba a kowacce jiha da kuma kowane mataki ko na mulki ko da kuwa a cikin gidanka ne kuma wannan ce tasa yanzu na ke alfahari da takawa da ƙarfi cewa ni mutumin Neja ne kafin wannan lokaci na Bago, kunya nake ji a ce ni ɗan jihar Neja ne, kamar dai yadda shugaban ƙungiyar Rahaji Empowerment Development, wato shugaban qungiyar samawa matasa aikin yi mai kula da jihohi 19 na Arewacin Nijeriya ya bayyana a yayin hira da manema labarai a birnin Kano, a ƙarshen makon da ya gabata.
Haka kuma, Bello Rahaji ya bayyana cewa a matsayinsa na shugaban wannan ƙungiya ta matasan Arewacin Nijeriya ya bayyana damuwarsa a kan yadda kashi 70 zuwa 80 na masu tafi da gwamnati ba matasa ba ne don haka akwai buƙatar asamu kyakkyauwar fahimta da ɗa’a ga dattawa da sauran magabata domin ta haka ne za’a samu dama matasa su zama jagori na gari da su inganta Nijeriya da al’ummarta.
A ƙarshe ya yaba wa Jihar Kano wanda ya ce mutanen Kano abin alfahari ne ga dukkanin jihohin Arewa musamman yadda suka karrama shi da lambar yabo ta ɗaya daga cikin jarimai da aka zaɓo masu ba da gudummawar al’umma wannan abun a yaba wa Kanawan Dabo ne a cewar Bello Rahaji, kuma yadda Kanawa suka iya siyasa ta hanyar tsayawa tsayin da ka su zaɓi wanda suka amince da shi wannan ya zame mana abun koyi a Jihar Neja, ya kuma zame mana abun koyi a Nijeriya a matsayinmu na matasa shugabannin gobe da ikon Allah.”
