Daga WAKILINMU
HortiNigeria ta ƙaddamar da gangami ga ‘yan jaridu kan yaƙi da tsutsar tumatir wacce ake kira Tuta absaluta a gidan Kwari, da ke ƙaramar hukumar Bunkure ta Jihar Kano.
A sakamakon mummunar illa da tsutsar Tuta absaluta take yiwa tumatir, HortiNigeria, wacce take samun tallafi daga ƙasar Neitherlands, ta ƙaddamar da wani gangami ga manema labarai kan yadda za a magance cutar Sharon wacce aka fi sani da Tuta absaluta.
A yayin gudanar da gangamin an nuna yadda aka tsara hanyoyi na yaƙar Tsutsar musamman kasancewar aikin ba na mutum ɗaya ba ne kan ɗaki ne sai an taru.
Feyikem Adurogbangba, Jami’ar yaɗa labarai a HortiNigeria, ta baiyana wa manema labarai cewa “wannan taron gangami an tsara shi ne don a faɗakarwa da kuma ilmantarwa ga masu ruwa da tsaki kan hanyoyi da kuma dabarun yadda za a magance wannan matsala.
“Domin ƙididdiga ta nuna ana asarar biliyoyin nairori a kan wannan cuta, kuma baya ga haka ana fargabar za’a sami ƙaranci tumatir idan ba a tashi haiƙan ba, to wannan yana daga cikin dalilan da suka sa muka samar da wannan gangami.”
Haka nan, shi ma Abdullahi Umar jam’i a IFDC ya ce, “abin da ya tara mu a yau muna so mu wayar wa da manoma kai a kan wannan cuta ta Sharon ko ibola wacce aka fi sani da Tuta absaluta.
“Saboda maganinta yana da tsada kuma in dai ta kama gona in ba’a kula ba tana jawowa manoma mummunar asara, don haka muna so manoma su san yadda za su magance wannan matsala da kuma yadda za su haɗa ƙarfi da ƙarfe su yi aiki tare da junan su domin tana buƙatar gaiya.
“Kuma muna kira ga manoman tumatir da su shiga ƙungiyoyin manoma musamman waɗanda ba su da ƙungiya don ta ƙungiya ne za su san me ke faruwa a halin da suke ciki.’
Taron dai ya sami halartar manoma na garin gidan Kwari da kuma ‘yan jaridu daga kafafen yaɗa labarai daban-daban daga gidajen jaridu, radiyo da talabishin.
