
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yaba wa jami’an tsaro bisa ƙoƙarin da suke yi da jajircewarsu wajen yaƙi da ayyukan ’yan bindiga a jihar.
Yabon na gwamnan ya biyo bayan nasarar da Sashen Daƙile Ayyukan Ta’addanci da Rikice-rikice, wato Violence Crime Response Unit – VCRU, na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ya samu na ƙwato shanu 329 da tumaki 175 daga hannun ’yan bindiga a dajin Gambanda da ke Ƙaramar Hukumar Gummi.
A wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya ce Gwamna Lawal ya bayyana cewa sabon ƙaimi da Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ke nunawa wajen yaƙi da matsalar tsaro alama ce mai ƙarfafa gwiwa kuma abin yabawa.
“Na yaba da ƙoƙarin dukkan jami’an tsaro da ke aiki a Jihar Zamfara, musamman Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara, saboda juriyarsu, jarumtarsu da kuma sadaukarwarsu wajen ƙwato shanu 329, tumaki 175, makamai da alburusai daga hannun ’yan bindiga,” in ji gwamnan.
Ya ƙara da cewa, jami’an tsaron sun fafata da ’yan bindigar tare da murƙushe su a dajin Gambanda da ke Ƙaramar Hukumar Gummi, lamarin da ya haifar da samun wannan gagarumar nasara.
Gwamnan ya bayyana cewa wannan nasara wata shaida ce ta irin sadaukarwar da jami’an tsaro ke yi duk da ƙalubalen da suke fuskanta daga masu aikata laifuka, tare da nuna muhimmiyar rawar da rundunar ’yan sanda ke takawa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Zamfara.
Ya ce, nasarar ƙwato dabbobin da makamai daga hannun ’yan bindiga ta nuna ƙwarewa da jarumtaka, tare da nuna irin shugabancin da Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Zamfara, CP Ahmed Muhammad Bello, ke bayarwa.
A cewarsa, jagorancin kwamishinan ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta tsaro da kuma ƙarfafa yaƙi da matsalar ’yan bindiga a jihar.
Gwamna Lawal ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bai wa dukkan hukumomin tsaro cikakken goyon baya domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’ar jihar.
