Sayen Vinicius babban haɗari ne ga Arsenal – Given

Spread the love

Tsohon mai tsaron ragar Newcastle United, Shay Given, ya gargaɗi Arsenal cewa yunƙurin sayen tauraron Real Madrid, Vinicius Junior, na iya jawo wa ƙungiyar babban haɗari.

Rahotanni sun bayyana cewa Arsenal na nazarin yiwuwar ɗaukar ɗan wasan na Brazil a wata yarjejeniya mai tsadar gaske, inda ake zargin kocin ƙungiyar, Mikel Arteta, ne ke jagorantar ƙoƙarin ganin an kawo shi zuwa arewacin birnin Landan.

An ce wannan yunƙuri na nuna sabon matsayi da Arsenal ta kai bayan lashe gasar Firimiya ta Ingila, tare da nuna irin ƙarfin kuɗin da ƙungiyar ke da shi a kasuwar musayar ‘yan wasa.

Sai dai, akwai fargabar cewa wannan ciniki na iya haifar da matsaloli ta fuskar kuɗi da kuma tsarin cikin gida na ƙungiyar.

Da yake magana da BOYLE Sports, Shay Given ya ce babu shakka Vinicius Junior na da ƙwarewar da Arsenal ke buƙata a ɓangaren kai hare-hare, amma ya yi gargaɗin cewa wannan ciniki babban caca ne.

Ya bayyana cewa kuɗin sayensa, albashinsa da sauran kuɗaɗen da za su biyo baya na iya kaiwa matakin da zai yi matuƙar nauyi ga Arsenal.

Given ya kuma tunatar da cewa ɗaya daga cikin manyan nasarorin da Arteta ya samu tun zuwansa filin wasan Emirates shi ne gina ƙungiya mai haɗin kai da ladabtarwa.

A cewarsa, Arteta ya fi ba da muhimmanci ga aiki tare da biyayya ga ƙa’idojin ƙungiya fiye da bai wa tauraro guda fifiko.

Ya yi gargaɗin cewa shigowar ɗan wasa mai irin wannan suna da tasiri na iya kawo cikas ga zaman lafiya da haɗin kan ɗakin sauya kaya na Arsenal.

Duk da haka, Given ya amince cewa manyan ƙungiyoyi kan ɗauki irin waɗannan haɗurran idan suna son ci gaba da samun nasara.

Ya ƙara da cewa, idan Arsenal ta samu nasarar ɗauko Vinicius Junior, wannan zai zama ɗaya daga cikin manyan cinikin musayar ‘yan wasa mafi ɗaukar hankali a shekarar nan.

By ukarofi

Leave a Reply