
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, ya caccaki tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar bisa cigaba da maimaita kiran Shugaba Bola Tinubu da sunansa na farko, yana mai cewa Tinubu dai shi ne Shugaban Ƙasa ko ma ta yaya abokan hamayya za su kira shi.
Shettima ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC gabanin zaɓen 2027 a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda ya kuma soki Atikun kan cigaba da tsayawa takarar shugaban ƙasa da kuma ƙalubalantar bayanin tattali daga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi.
Shettima ya ce kasantuwar Tinubu a matsayin shugaban ƙasa yana nan a dokance ba tare da canji ba ko ma da me Atiku zai kira shi don haka babu abin da zai sauya daga matsayin nasa.
“Wajibi ne waɗanda suka zo ƙoƙarin samar da daidaito su zo da kyawawan hannaye. Za ka iya kiran sa Bola. Idan ka ga dama ka kira shi Adekunle. Amma haƙiƙanin gaskiya shi ne shugaban ƙasar kuma kwamandan rundunar tsaron tarayyar jamhuriyar Nijeriya,” inji Shettima.
Haka kuma, Mataimakin Shugaban Ƙasar ya soki yunƙurin Atiku na son zama shugaban ƙasa a lokuta mabambanta, inda ya kamanta shi da tsohon firaministan Kenya, Raila Odinga, wanda ya sha tsaya wa takarar shugaban ƙasa a lokuta da dama amma bai samu.
Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da kaɗa gangar siyasar zaɓukan 2027, inda Tinubu da Shettima ke fatan koma wa karagar mulki a karo na biyu, yayin da Atiku na ADC da su Peter Obi ke gogayya da su a muƙamin.
