AI na cikin manyan batutuwan da aka tattauna a taron Frankfurt Book Fair

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Duniyar littafi na canzawa a hankali, amma wasu sauye-sauyen sukan zo da tambayoyin da ba za a iya kauce musu ba. Yayin da fasahar AI ke ƙara shiga cikin rubutu da wallafe-wallafe, masana’antar littafi ta fara fuskantar tambayoyi kan abin da wannan fasaha za ta sauya da kuma abin da ya kamata a kare.

A ranar, Laraba 7 ga Oktoba, an buɗe Frankfurt Book Fair karo na 78 a Jamus, inda marubuta, masu wallafa, masu fassara da sauran masu ruwa da tsaki a duniyar littafai suka taru, inda taron zai ci gaba har 11 ga Oktoba.

AI na daga cikin manyan batutuwan da suka mamaye shirin taron bana. Shafin Frankfurt Book Fair ya ce fasahar tana ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin batutuwan da ke tsara tattaunawar masana’antar wallafe-wallafe a bana.

Daga cikin shirye-shiryen da aka tanada akwai AI in Academic Publishing da kuma AI in Culture: Truth or Fiction?, wanda zai duba tasirin AI kan littattafai, ilimi, koyo da al’adu, musamman a lokacin da bayanan ƙarya ke iya yaɗuwa cikin sauri.

Haka kuma, akwai tattaunawa kan yadda ake sa littattafai su samu masu karatu a zamanin binciken AI, da kuma yadda masu wallafa ke amfani da fasahar wajen sauya wasu daga cikin hanyoyin da ake gudanar da masana’antar.

Saidai ba AI kaɗai ce ke cikin shirin taron ba. Frankfurt Book Fair ta kuma sanya batutuwan dimokuraɗiyya, haƙƙin ɗan Adam, ‘yancin wallafawa da kuma yaɗuwar bayanan ƙarya cikin muhimman abubuwan da za a tattauna.

Akwai kuma marubuta da masana daga ƙasashe daban-daban da za su halarci taron, yayin da Jamhuriyar Czech take a matsayin baƙuwar girmamawa ta bana.

Sai dai yayin da masana’antar ke ƙoƙarin fahimtar yadda za ta yi amfani da AI, akwai tambaya mai muhimmanci da ke zukatan marubuta ta cewa, idan na’ura za ta iya samar da rubutu cikin sauri, mene ne zai sa muryar marubucin ta ci gaba da kasancewa ta musamman?

Yayin da Frankfurt Book Fair ke buɗe ƙofofinta a wannan makon, wannan ce daga cikin tambayoyin da duniyar littafi take ƙoƙarin amsawa.

By ukarofi

Leave a Reply