Hukumar NASPHFIRA a Nasarawa ta fara tantance da rijistar asibitoci masu zaman kansu

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Hukumar kula da asibitoci da cibiyoyin lafiya masu zaman kansu ta Jihar Nasarawa wato (NASPHFIRA) ta fara tantancewa da rijistar masu asibitoci da ke zaman kansu dake aiki a jihar.

Babbar sakatariyar hukumar, Dakta Nana Awaya Emeribe ce ta bayyana hakan a ranar Talata yayin da ake cigaba da gudanar da aikin tantancewar a ofishin hukumar da ke Lafia.

A cewarta an tsara aikin ne domin samar da ingantaccen bayanan dukkan ƙwararrun masu zaman kansu a fannin lafiya, tabbatar da cancantar su ta fuskar sana’a, da kuma tabbatar da cewa kwararru masu lasisi da cancanta kaɗai ne aka bari su gudanar da aikin kiwon lafiya a jihar.

Tace shirin zai taimaka wajen tsaftace ɓangaren lafiya mai zaman kansa, kawo ƙarshen ayyukan bogi, da kuma tabbatar da ingantaccen kiwon lafiya ga al’ummar jihar.

Ta yi gargaɗin cewa duk wata cibiyar lafiya mai zaman kanta da ke aiki ba tare da ingantacciyar rijista da lasisi ba za a rufe ta a karshen wannan aikin, tana mai jaddada cewa zamanin gudanar da aikin lafiya mai zaman kansa ba tare da ƙa’ida ba a Jihar Nasarawa ya zo ƙarshe kana tace a shirye hukumar yake ya dau ƙwararan matakai don hukunta waɗanda za su ki bayyana a hukumar don tantancewa da rajistar.

Shugabar ta NASPHFIRA Dokta Nana Awaya Emeribe ta kuma yi kira ga duka masu asibitoci da ke zaman kansu da har yanzu ba su gabatar da kansu don tantancewar da rajista ba da su yi hakan ba tare da ɓata lokaci ba, tana mai tabbatar musu da cewa za a gudanar da aikin cikin gaskiya da sauƙi da kuma adalci.

By ukarofi

Leave a Reply