Ɓarawo ya maƙale wajen satar wayar wuta a Kebbi

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Rana ta ɓaci ga wani ɓarawon wayar wutar lantarki a ƙauyen Sabon garin Goru da ke wajen garin Birnin Kebbi inda ya je satar waya aka mayar da wuta.

Malam Usman Goru ya labartawa wakilin mu da cewa da safiyar Talatar da ta gabata ne suka wayi gari da wani abin al’ajabi inda suka hango wani mutum maƙale a saman wayar wutar lantarki da biyo ta ƙauyen.

Bayanin da wakilin mu ya kalato ya nuna ɓarawon wanda daman sananne ne a yankin ya hau saman wayar ne da zummar katse wayoyin jim kaɗan bayan an ɗauke wuta da ƙarfe goma na daren ranar Litinin, bisa rashin sa’a sai aka mayar da wuta inda ja shi sai dai bai mutu ba amma a haka ya maƙale har gari ya waye.
Sai dai bayan gari ya waye da aka kira yan sanda da jami’an hukumar lantarki suka saukar da shi, ba tare da la’akari da yanayin da ya ke ciki ba al’umma sun fusata inda suka nemi su hallaka shi amma dai jami’an yan sanda suka hana.

An dai garzaya da shi a asibiti don duba lafiyar sa saboda raunuka da ya samu sanadiyyar jan da wutar ta yi masa.

By ukarofi

Leave a Reply