El-Rufa’i: Shaida ya yi zargin ware Dala 600,000 don dakatar da binciken EFCC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wani shaida a shari’ar rashawa ta tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya yi zargin cewa an ware Dala 500,000 da wani Dala 100,000 domin bai wa jami’an Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) a matsayin cin hanci saboda su dakatar da bincike akan wasu kamfanoni a shari’ar da ake masa.

An gudanar da zaman ne na tsawon sa’o’i tara, wanda Mai Shari’a Darius Khobo na Babbar Kotun Jihar Kaduna ya jagoranta a ranar Talata, kana ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranakun 30 ga Nuwamba da kuma 1 ga Disamba, 2026. Tsohon gwamnan ya kasance da gurin tsayuwar shaida a kotun har aka kammala zaman.

Shaidan mai suna Segun Kayode, wanda babban jami’i ne na Hukumar Tsaro ta Farin kaya (DSS) da nazarin fasahar dijital, ya yi wannan zargi ne a ranar 13 ga Oktoba, 2026 yayin bayar da ba’asin abin da ya sani kan shari’ar. Ya shaida wa kotun cewa shi da ‘yan tawagarsa sun gudanar da nazari kan rahotannin kira da ɗaukar murya da suka samo yayin bincike, bayan buƙatar haka a hukumance daga Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC).

Ya ce, bincikensu ya haɗa da wasu lambobin waya na El-Rufa’i da wasu makusantansa da ake zargi, ciki har da Jimi Lawal, AU Mustafa, Ahmadu Sule, Sam Darwish da wasu. A cewar shaidan, bayan amincewar Darakta-Janar na DSS, daraktan yaƙi da laifukan ta’addanci ya umarci tawagarsa da su gudanar da sharhin kiran wayar da suka gudana a tsakanin mutanen. Ya bayyana cewa sharhin nasu ya gano an samu kiran waya akai-akai tsakanin El-Rufa’i da wansa Bashir El-Rufa’i da wani Sam Darwish tsakanin 25 da 28 ga Oktoba, 2025.

Ya ce, sun gano cewa an samu wata tattaunawa a tsakaninsu akan neman a dakatar da binciken EFCC akan wani kamfani mai suna Singularity da neman a rufe shi a Nijeriya da Mauritius, wanda ya kai ga wani bincike daga Sashen Leƙen Asirin Kuɗi na Nijeriya (NFIU) a Mauritius.

Har ila yau, Kayode ya yi zargin cewa, rahoton ya ƙunshi umarnin cewa Sam Darwish, Gimi Lawa da AU Mustafa sun nemi dakatar da EFCC binciken IHS, wanda kamfanin canjin kuɗi ne na New York. Sannan an gano cewa an ware $500,000 da wani $100,000 ga jami’an EFCC domin su dakatar da binciken nasu akan shari’ar.

By Babaji

Leave a Reply