Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Hukumar dake yaƙi da cutar sida a jihar Katsina, (KATSACA) haɗin guiwa da gidauniyar Safe Space Humanitarian Initiative (SASHIN) ta bada tallafin kayan haihuwa da gangamin wayar da kai kan cutar sida ga mata 200 a ƙaramar hukumar Ingawa da ke jihar Katsina.
Da yake jawabi a wajen taron, shugaban hukumar KATSACA, Dr. Bala Nuhu Kankia, (Sadaukin Kankia) ya ce hukumar ta daɗe tana ayyukan alkhairi tare da wayar da kan al’umma kan cutar sida a jihar Katsina, wanda duk ƙaramar hukumar da KATSACA ta je tana ba mata 100 tallafin kayan haihuwa da kuma kuɗaɗe, amma a ƙaramar hukumar Ingawa an ba da 200 saboda gudunmawar da matar gwamnan jihar Katsina, Hajia Zulaihat Dikko Umaru Raɗɗa ta ƙara mata 100 ƙarƙashin gidauniyar SASHIN da take jagoranci.
A cewarsa, burin hukumar KATSACA shi ne kawar da cutar sida baki ɗaya a jihar Katsina, wanda ya ce ya zuwa yanzu sun bada tallafi ga mata sama da 3,000 a ƙananan hukumomi 11.
Ya bayyana cewa ya zuwa yanzu mutane 20,000 a jihar Katsina daga sassan ƙananan hukumomi 34 na jihar, suna fama da cutar sida, amma kuma sun shawo kan matsalolin inda sama da mutane 18,000 ke shan magani kan lokaci, wanda ya ce ya zuwa yanzu Asibiti 41 na Katsina suna zuwa ana duba su tare da ba su magunguna kyauta da kuma wayar da kan su don dakile yaɗuwar cutar baki ɗaya.
Dr Bala Kankia ya ce, Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi, ta tabbatar da cewa, ana son samun kashi 95% ma su shan magunguna wanda ya zuwa yanzu a jihar Katsina suna da kashi 85% ma su shan magunguna, inda ya ayyana cewa ya tabbatar da cewa nan da shekaru 3 jihar Katsina za ta samu kashi 95% na masu shan magunguna.
Ita ma da take jawabi lokacin, Uwargidan Gwamnan jihar Katsina, kuma Shugabar gidauniyar Safe Space Humanitarian Initiative (SASHIN) Hajia Zulaihat Dikko Umaru Radda, ta ce ta ji dadi da Hukumar KATSACA take tarukan wayar da kai ga al’ummar jihar Katsina, musamman Mata game da Cutar Sida.
Ta ce ta dalilin haka ne ta ƙara adadin tallafin kayan haihuwa da na kuɗi ga mata 100 ƙarƙashin gidauniyar SASHIN, wanda suka za ma 200 idan aka hada da na KATSACA 100, domin tallafa ma su tare da wayar ma su da kai.
A cewarta, tunda farko gidauniyar SASHIN, koyaushe burinta tallafawa al’umma musamman masu karamin ƙarfi da suka fito a jihar Katsina, da suka haɗa da masu cutar sikila, da kansa, da sauran wasu tallafi daban-daban da suka shafi inganta lafiya da sauran su.
