Buni ya raba babura 160 ga dakarun tsaron dazuzzuka da ke jihar

Spread the love

Daga SANI GAZAZ CHINADE a Damaturu

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ƙaddamar da raba babura 160 da sauran kayan aikin tsaro ga masu gadin dazuzzuka na ƙasa da ke jihar domin inganta ƙarfin aikinsu da kuma ƙarfafa ƙoƙarin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Gwamnan, wanda Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG), Dr. Mohammed Goje, ya wakilta, ya kuma amince da raba rigunan kare ruwan sama guda 900, takalman tsaro (boots) guda 900, barguna 900, fitilun hannu 900, da kuma gidan sauro guda 900 ga ma’aikatan.

An tanadi waɗannan kayan ne domin tallafawa masu gadin dazuzzuka su 886 da suka kammala horo tare da tura su wurare daban-daban a faɗin jihar.

Da yake jawabi a wajen bikin kaddamarwar a gidan gwamnati da ke Damaturu, Goje ya ce wannan mataki yana nuna ƙudirin gwamnatin jihar na samar wa ma’aikatan kayan aikin da suka dace domin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

“A madadin mai girma Gwamnan Jihar Yobe, ina jin daɗin da kuma alfaharin sake ƙaddamar da raba waɗannan muhimman kayayyaki a hukumance domin inganta ayyuka da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar” in ji Goje.

A nasa jawabin, mashawarci na musamman ga Gwamna Mai Mala Buni kan harkokin tsaro, Birgediya Janar Dahiru Abdulsalam (mai ritaya), ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ce ta amince da kafa shirin masu gadin dazuzzuka, yayin da jihar Yobe ta samar da rukunin farko na sabbin ma’aikata 1,000 a ƙarƙashin shirin gwaji.

A cewarsa, an ɗauki sabbin ma’aikatan ne daga ƙananan hukumomi bakwai, waɗanda suka haɗa da Gulani, Gujba, Damaturu, Tarmuwa, Bursari, Yunusari, da Geidam.

Ya ce mutane 886 ne suka kammala horonsu na farko cikin nasara a watan Disambar bara, kafin daga bisani su sake samun ƙarin horo tare da Sojojin Najeriya domin ƙarfafa ƙwarewarsu wajen gudanar da aiki.

Abdulsalam ya bayyana cewa samar da baburan na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na samar wa masu gadin kayan aikin da za su ba su damar gudanar da sintiri yadda ya kamata a yankunan dazuzzuka da kuma inganta ayyukan tsaro.

Ya ƙara da cewa an tsara wannan shiri ne domin taimaka wa hukumomin tsaro wajen tabbatar da kasancewarsu yadda ya kamata a yankunan da ba a samun cikakken ikon gwamnati, tare da tunkarar barazanar tsaro.

Shi ma kwamandan rundunar soja ta ’27 Task Force Brigade’, Birgediya Janar M.S. Mukhtar, ya yaba wa Gwamna Buni bisa samar da babura da sauran muhimman kayan aiki ga jami’an tsaron dazuzzuka da ke aiki a ƙarƙashin rundunar su a jihar Yobe.

Mukhtar ya bayyana wannan tallafi a matsayin matakin da zai ƙara ƙarfin aikin rundunar, ta hanyar inganta yadda jami’an ke zirga-zirga, zagayawa don sintiri, da kuma ikon ɗaukar matakin gaggawa.

Ya ce kayan aikin za su ƙarfafa ayyukan yaƙi da ta’addanci, ayyukan ‘yan fashi, da sauran laifuka a faɗin jihar.

By ukarofi

Leave a Reply