
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa, akwai yiwuwar ya haƙura da zuwa wasu tarukan yaƙin neman zaɓe a wasu jihohi yayin da yake neman al’ummar Nijeriya su sake zaɓar sa a karo na biyu a zaɓen 2027, saboda akwai buƙatar ya kula da al’amuran shugabanci.
Shugaban ya yi wannan isharar ne yayin da yake magana a taron ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓensa na Jam’iyyar APC a ɗakin taro na Banquet Hall da ke Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja, ranar Laraba.
Tinubu ya ce, an shawarce shi da kada ya bari yaƙin neman zaɓe ya ɗauke hankalinsa daga nauye-nauyen da ke kansa na jagorancin ƙasar, inda ya ƙara da cewa Nijeriya tana buƙatar kulawarsa a halin yanzu. Ya kuma ce, ta yiwu nauye-nauyen da ke ofishinsa ba za su ba shi damar ya riƙa rakiya ga ‘yan kwamitin yaƙin neman zaɓen nasa ba a matakin kowace jiha da ƙaramar hukuma.
A yayin ƙaddamar da kwamitin, ƙarƙashin jagorancin Sanata Abdulaziz Yari a matsayin darakta-janar, Shugaba Tinubu ya bayyana hakan a matsayin abin da ke wakiltar sabunta ƙoƙarin hidimta wa ‘yan Nijeriya da nauye-nauye masu tarihi da aka yarje akan jam’iyyar mai mulki.
Kazalika, Tinubu ya ce ana sa ran kwamitin zai isar da matakin hangen nesan gwamnatinsa, nasarori da ajandar masu zaɓe a sassan ƙasar yayin da yake jagorantar yaƙin neman zaɓe gabanin zaɓukan 2027.

