Gidajen mai a Kebbi sun rufe sanadiyyar rage farashi

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Akwai alamar an je gyaran targaɗe an karye saboda yanzu haka al’amurra sun tsaya cik a waɗansu sassa na Nijeriya sanadiyyar rage farashin mai na naira sittin na wata ɗaya da gwamnatin ta sanar.
A jihar Kebbi wakilin Jaridar Blueprint Manhaja ya zagaya waɗansu wurare, ya tarar da gidajen mai a rufe sai dai kaɗan daga cikin su da suka buɗe sai dai ba nan gizo ke saƙa ba saboda maimakon a sami sauƙi daga inda aka fito yanzu ana sayar da shi naira 1500 zuwa da ɗari biyar da hamsin.
Wani manajan da bai so a bayyana sunan sa ba ya ce mai gidan sa ne ya umarce shi da ya rufe gidan mai har sai yadda hali ya yi saboda ba za su iya rage kuɗi ba su faɗi, don man da ke wajen su yanzu mai tsada ne idan suka rage kudi za su fadi.
Gidan man DIZA da ke anguwar Gwadangaji cikin garin Birnin Kebbi shi ma a rufe ya ke inda daya daga cikin ma’aikatan gidan ya bayyana cewa mai ne ya ƙare kuma daga yanzu kowane lokaci suna sa ran a kawo kuma idan an kawo za su cigaba da sayarwa.

Wani ɗan acaba Mustapha Musa ya bayyanawa wakilin mu da cewa sanadiyyar rage kuɗin mai da aka ce an yi waɗansu gidajen mai sun rufe waɗanda kuma suka buɗe maimakon su rage sai suka ƙara kuɗin lita daga naira 1400 da talatin sai suka mayar naira 1500 zuwa da 50.
Wani ma’aikacin gwamnatin jihar Kebbi da ke zama a garin Jega Malam Muhammed Aminu ya bayyana cewa wannan ragin ya cutar da al’umma saboda maimakon a sami sauƙi sai abin ya zo da wahala.
Ya ƙara da cewa yanzu ai ba maganar zuwa wajen aiki saboda direbobi sun ajiye motoci waɗansu kuma sun ƙara kuɗin mota.

Yanzu haka dai titunan cikin gari da kuma manyan hanyoyi da suka haɗa garuruwa kamar an share saboda ba motoci da ke zirga-zirga, ta ko ina babu sauƙi ga ɗan Nijeriya sai dai addu’ar Allah ya kawo mafita.

By ukarofi

Leave a Reply