Daga marubuta 2,000 zuwa 25: National Book Awards ta bayyana waɗanda suka rage a gasar 2026

Spread the love

Daga AISHA ASAS

A duniyar adabi, ba kowane littafi ne yake samun damar tsayawa a inda duniya za ta fara kallonsa da wata irin kulawa ba. Amma idan aka rage dubban littattafai zuwa wasu kalilan, sunayen marubutan da suka rage sukan fara ɗaukar wata sabuwar ma’ana.

Haka abin ya faru a gasar National Book Awards ta 2026, inda aka bayyana ‘yan takarar ƙarshe 25 a ranar Talata, 6 ga Oktoba, bayan alkalai sun tantance kusan littattafai 2,000 da aka wallafa a bana.

An raba waɗanda suka rage zuwa rukuni biyar: Fiction, Nonfiction, Poetry, Translated Literature da Young People’s Literature. A cikin Fiction akwai fitattun marubuta irin su Edwidge Danticat, Valeria Luiselli da Julián Delgado Lopera, yayin da wasu daga cikin sauran rukunan suka haɗa da sunaye irin su Karl Ove Knausgaard da Fady Joudah.

Abin da ke ƙara wa jerin sunayen muhimmanci shi ne cewa ba batun adabin nishaɗi kawai ake gani a cikin littattafan ba. Wasu daga cikinsu sun taɓo batutuwan da suka shafi yaƙi, adalci, jinsi, tarihi, kurkuku da kuma rikice-rikicen da ke cikin al’umma.

Wannan ne ya sa irin waɗannan lambobin yabo suke da muhimmanci ga marubuci. Domin ba kawai suna ne ake nema a jikin wata kyauta ba; wani lokaci ana neman amsar tambayar da ta fi girma, ta shin abin da marubucin ya rubuta na iya kama da wani abu daga cikin rayuwar mutane?

A bana, marubutan 25 ne kawai suka rage daga cikin ɗimbin waɗanda aka duba, kuma waɗanda za su lashe kyaututtukan za a bayyana su a ranar 18 ga Nuwamba a wani biki da za a gudanar a Manhattan.

Daga nan ne za a ga waɗanne littattafai ne za su bar wannan gasar da kyautar, amma tun kafin a kai wannan matakin, sunayen waɗannan marubutan 25 sun riga sun samu abin da kowane marubuci ke nema, wato damar da aikin da ya rubuta ya kai ga idon duniya.

.

By ukarofi

Leave a Reply