FIFA ta kira taron gaggawa yayin da matsin lamba ke ƙaruwa kan buƙatar tsige Infantino

Spread the love

Shugaban Hukumar ƙwallon ƙafa ta Duniya (FIFA), Gianni Infantino, ya kira taron gaggawa na manyan jami’an hukumar a birnin Rabat na ƙasar Moroko, yayin da ake ci gaba da fuskantar matsin lamba kan ya sauka daga muƙaminsa saboda wata taƙaddama da ta shafi shirin shigar da masu zuba jari masu zaman kansu cikin harkokin gudanar da gasar FIFA.

Taron na ranar Laraba ya haɗa da Sakatare Janar na FIFA, Mattias Grafstrom, da mambobin kwamitin gudanarwar hukumar domin nazarin rikicin da ya biyo bayan shirin kafa kamfanin FIFA Forward Enterprise (FFE), wanda daga bisani aka soke.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin shugabanci ke ƙara ta’azzara a FIFA, inda ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Turai (UEFA) ta bayyana a hukumance cewa ta daina amincewa da shugabancin Infantino.

Taƙaddamar ta samo asali ne bayan rahotanni sun nuna cewa FIFA na shirin kafa wani kamfani mai zaman kansa mai suna FIFA Forward Enterprise (FFE) domin kula da harkokin kasuwanci da gudanar da gasannin hukumar.

A ƙarƙashin wannan tsari, FIFA ta shirya sayar da kashi 20 cikin ɗari na hannun jarin kamfanin ga masu zuba jari masu zaman kansu domin samar da ƙarin kuɗaɗen gudanar da harkokin ƙwallon ƙafa ta duniya.

Sai dai shirin ya fuskanci kakkausar adawa daga ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na nahiyoyi daban-daban, waɗanda suka yi gargaɗin cewa hakan na iya raunana ’yancin FIFA da kuma ikonta kan manyan gasanninta.

Sakamakon wannan matsin lamba, FIFA ta sanar a ƙarshen makon da ya gabata cewa ta yi watsi da shirin.

By ukarofi

Leave a Reply