
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An fara gudanar da karatun Musabƙar Al-Ƙur’ani Mai Girma na Sarki Abdulaziz na Ƙasa-da-ƙasa karo na 46 a Makkah, Saudiyya, inda aka samu jimillar ‘yan takara 334 da suka ƙunshi maza da mata daga ƙasashe 133 da suka halarta.
Rahotanni sun bayyana cewa, a ranar Alhamis aka fara gasar a ƙarƙashin jagorancin Masallatai biyu Masu Alfarma na Sarki Salman, wadda Ma’aikatar Harkokin Addinin, Kira da Kariya ta ƙasar ta shirya.
A ranar 6 ga watan Rabi Al-Awwal (19 ga Agusta) ne za a kammala gasar, wadda ta samu adadin ‘yan takara mafi yawa tun bayan fara ta, lamarin da ke nuna ƙara samun karɓuwarta acikin ƙasashen Musulmi.
A cewar masu shiryawa, ana gudanar da gasar ta shekara-shekarar ne da nufin kwaɗaitar da matasan musulumi hardar Al-Ƙur’ani, fahimtarsa da biyayya ga karantarwarsa.
Haka kuma, gasar na nuna aiki tuƙuru da Saudiyya je yi na ganin ta girmama Al-Ƙur’ani Mai Girma da kuma karrama waɗanda suka sadaukar da kawunansu wajen hardace shi da fahimtar ma’anoninsa.
A wannan shekarar akwai gasa daban-daban da aka shirya wa ɗalibai mata, inda za su tarukansu a otel ɗin Makkah Hilton Hotel & Convention.
Kazalika, za a gudanar da zango na ƙarshe na tsagin maza da kuma tarin rufewa a Babban Masallacin Makkah.
An raba gasar zuwa gida biyar, inda ‘yan takarar ke gasar lashe Riya 10,260,000, wato kwatankwacin biliyan N3.7, mafi adadin kuɗi da aka taɓa samarwa a tarihin gasar.
