Daga MUHAMMAD MUJITABA a Kano
An ci gaba da gudanar da addu’o’i da tunawa da marigayi Malam Adamu, tsohon direba da aka bayyana a matsayin mutum mai kyakkyawar mu’amala, zaman lafiya da kuma bayar da gudunmawa ga al’umma, shekaru 11 bayan rasuwarsa.
Iyalan marigayin, ‘yan uwa da abokan arzikinsa sun ce har yanzu ba su manta da shi ba, kuma suna ci gaba da yi masa addu’a tare da tuna kyawawan halayensa.
An haifi Malam Adamu a ranar 2 ga Fabrairu, 1920, sannan ya rasu a ranar 17 ga Janairu, 2015.
Da yake jawabi a wajen taron addu’ar, shugaban masu gudanar da addu’ar, Alhaji Ibrahim, wanda aka fi sani da Mobile, ya ce marigayin ya yi gwagwarmaya wajen neman halal a wurare daban-daban, ciki har da Kamfanin Yaro Gambo Motor.
Inji shi, marigayin ya rasu ya bar ‘ya’ya biyar da jikoki 28, yana mai cewa za su ci gaba da shirya irin wannan taron addu’a domin tuna shi.
Ya kuma jaddada muhimmancin ci gaba da yi wa iyaye da sauran magabata addu’a, musamman bayan sallolin farilla da nafila da sauran ayyukan alheri.
