Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Mutane biyu sun rasa rayukansu bayan ruwan sama mai ƙarfi ya haddasa ambaliya a wasu sassan birnin Damaturu, babban birnin Jihar Yobe.
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA) ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Talata.
An bayyana waɗanda suka rasu da suna Isa Haruna, mai shekara 38, jami’in tsaro da aka fi sani da Mallam Matari, da kuma Abba Kyari, mai shekara 18, wanda rahotanni suka ce ya nutse a yankin Pompomari.
A cewar SEMA, ambaliyar ta afku ne a unguwannin Malari, Pompomari da wasu yankunan da ke maƙwabtaka da su bayan ruwan sama mai ƙarfi da aka yi da sanyin safiyar ranar Litinin.
Hukumar ta ce tawagar bincike da ceto ta haɗa kai da Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Yobe domin kai ɗauki bayan samun kiran gaggawa, amma da suka isa wurin sun tarar da mutanen sun riga sun rasu.
An kwashe gawarwakin zuwa Sashen Gaggawa na Asibitin Kwararru na Janar Sani Abacha da ke Damaturu.
SEMA ta yi kira ga mazauna jihar, musamman waɗanda ke zaune a yankunan da ambaliya ke yawan afkuwa, da su ƙara taka-tsantsan a lokacin damina.
Hukumar ta kuma shawarci jama’a da su guji tafiya, wasa ko tuka ababen hawa a kan hanyoyin da ruwa ya mamaye, magudanan ruwa da rafuka.
Haka kuma, ta buƙaci iyaye da masu kula da yara da su hana yara kusantar koguna, rafuka, magudanan ruwa da wuraren da ambaliya ta mamaye, musamman ganin cewa makarantu na hutun ƙarshen zangon karatu.
