Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Sarkin Maganin Gargajiya na Jihar Kano, Dakta Rabilu Muhammad, ya naɗa Alhaji Jamilu Lamir Jibrin a matsayin sabon Sarkin Maganin ƙaramar Hukumar Fagge, bayan rasuwar mahaifinsa, marigayi Dakta Lamir.
An gudanar da bikin naɗin ne a fadar Sarkin Maganin da ke Kano a ranar Laraba, inda Sarkin ya shawarci sabon Sarkin Maganin da ya yi koyi da kyawawan halayen mahaifinsa na ƙaunar al’umma, karamci da biyayya ga masarautar maganin gargajiya ta Jihar Kano.
Da yake jawabi a madadin iyalan marigayin, Alhaji Mukhtar Lamir ya gode wa Sarkin Maganin Kano da majalisarsa bisa wannan naɗi.
Ya ce, “Muna matuƙar godiya ga Dakta Rabilu Muhammad da ya amince Jamilu ya gaji sarautar mahaifinsa.”
A nasa jawabin, sabon Sarkin Maganin Fagge, Alhaji Jamilu Lamir Jibrin, ya bayyana farin cikinsa da godiyarsa ga Allah bisa wannan matsayi, tare da gode wa Sarkin Maganin Kano da daukacin masarautar.
Ya ce zai yi iya ƙoƙarinsa wajen bin sawun mahaifinsa ta fuskar kyautata wa al’umma da kuma hidimar masarautar.
“Da yardar Allah zan ci gaba da bin tafarkin mahaifina wajen yi wa al’umma hidima da kyautata musu. Ina kuma kira ga matasa da su kasance masu biyayya ga iyaye da dattijai tare da zaman lafiya da kowa,” inji shi.
Ya ƙara da cewa kamfanin haɗa magungunan gargajiya na LAMJIB, wanda mahaifinsa ya kafa, za su ci gaba da bunƙasa shi domin ya zama sananne ba kawai a Nijeriya da Afirka ba, har ma a faɗin duniya.
Bikin ya samu halartar masu riƙe da sarautun gargajiya, malamai da ɗimbin jama’a, ciki har da Sarkin Shinfiɗa na Maganin Gargajiya na Kano, Dakta Sani Muhammad Tsamiya Babba, da sauran mambobin majalisar Sarkin Magani.
