Majalisar Dokokin Katsina ta nemi daidaita kuɗin makarantu masu zaman kansu

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina 

Majalisar Dokoki a Jihar Katsina ta yi kira ga ɓangaren zartarwa na gwamnati da ta samar da tsarin da zai daidaita yadda makarantu masu zaman kansu da na al’umma ke gudanar da ayyukansu, musamman kan yawan kuɗin makaranta da kuma tsarin gudanarwarsu.

Hakan ya biyo bayan   kudiri da ɗan majalisa mai wakiltar Katsina, Alhaji Aliyu Abubakar Albaba, ya gabatar, inda ya nuna damuwa kan yawan ƙarin kuɗin makaranta ba tare da ingantaccen tsari na sa ido ba.

A zaman Majalisar da Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura, ya jagoranta, an kuma buƙaci gwamnatin jihar ta gina aƙalla manyan hanyoyi biyu tare da samar da fitilun kan titi da magudanan ruwa a wasu yankuna na ƙaramar Hukumar Malumfashi. ƙudirin ya fito ne daga ɗan majalisa mai wakiltar Malumfashi, Alhaji Aminu Ibrahim, wanda ya ce sabbin hanyoyin za su inganta tattalin arziki, sauƙaƙa zirga-zirga da kuma  inganta samun damar zuwa makarantu da cibiyoyin lafiya.

By ukarofi

Leave a Reply