Jihar Katsina ta cika shekara 39 da kafuwa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Jihar Katsina wanda tsohon shugaban ƙasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya ƙirƙira da Jihar Bayelsa a rana guda yau ta cika shekara 39 da ƙirƙira

A saƙon sa ga al’ummar Jihar Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya taya al’ummar jihar murnar cika shekaru 39 da kafuwar jihar, yana mai cewa Katsina na ci gaba da tafiya bisa manufofin ci gaba, tare da gina tubalin samun ingantaccen tsaro, wadata da ƙaruwar tattalin arziki

A cikin saƙon da babban sakataren yaɗa labaransa, Ibrahim Kaula Mohammed, ya fitar a ranar 23 ga Satumba 2026, Gwamna Raɗɗa ya ce bikin cikar jihar shekaru 39 wata dama ce ta tunawa da jajircewa da gudummawar al’ummomin da suka gabata wajen gina Katsina.

Dikko ya ce ajandar gwamnatinsa ta “Building Your Future” ta mayar da hankali kan fannoni da suka haɗa da tsaro, ilimi, lafiya, noma, samar da ababen more rayuwa, ƙarfafa tattalin arziki, gyaran hukumomin gwamnati da ci gaba mai ɗorewa.

Ya bayyana cewa ana ƙoƙarin kusantar da ayyukan gwamnati zuwa ga al’umma, tare da zuba jari a fannonin ilimi, kiwon lafiya, noma, hanyoyi da sauran muhimman abubuwan more rayuwa a faɗin ƙananan hukumomin jihar.

Gwamnan ya jaddada muhimmancin tallafawa matasa, mata, manoma, ’yan kasuwa da ƙananan sana’o’i, domin ƙara musu damar dogaro da kansu da kuma samar da ayyukan yi

Dangane da tsaro, Gwamnan ya amince cewa har yanzu akwai ƙalubale a wasu al’ummomin jihar, yana mai cewa gwamnati za ta ci gaba da aiki tare da hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya, shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki domin kare rayuka da dukiyoyi da kuma neman dorewar zaman lafiya.
Gwamna Raɗɗa ya kuma yi kira ga al’ummar Katsina da su ɗauki ci gaban jihar a matsayin nauyin kowa, ba tare da la’akari da bambancin siyasa, addini ko zamantakewa ba.

Ya yaba wa tsoffin shugabanni, sarakunan gargajiya, ma’aikatan gwamnati, jami’an tsaro da sauran ’yan Katsina da suka bayar da gudummawa wajen ci gaban jihar tun bayan kafuwarta.

Malam Dikko ya ce gwamnati za ta ci gaba da aiwatar da shirye-shiryenta, kammala ayyukan da ake kan ginawa, ƙarfafa hukumomin gwamnati da faɗaɗa damar ci gaba ga al’umma.
Gwamnan ya kuma yi addu’ar samun zaman lafiya, haɗin kai da wadata ga Jihar Katsina, tare da taya daukacin ’yan jihar, ciki har da waɗanda ke zaune a ƙasashen waje, murnar cikar jihar shekaru 39.

An gudanar da addu’o’i a masallatai da gabatar shirya taron gabatar da kasida wanda ake sa ran Wazirin Katsina Sanata Ibrahim Ida zai gabatar a babban ɗakin taron na gidan gwamnatin Katsina.

By ukarofi

Leave a Reply